First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
تَبَارَكَ الَّذِي بِيَدِهِ الْمُلْكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Hausa
(Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannunSa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko
ne a kan kome.
|
Ayah 67:2 الأية
الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا
ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ
Hausa
Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga
cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.
|
Ayah 67:3 الأية
الَّذِي خَلَقَ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ طِبَاقًا ۖ مَّا تَرَىٰ فِي خَلْقِ الرَّحْمَٰنِ
مِن تَفَاوُتٍ ۖ فَارْجِعِ الْبَصَرَ هَلْ تَرَىٰ مِن فُطُورٍ
Hausa
Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga
goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga
wata ɓaraka?
|
Ayah 67:4 الأية
ثُمَّ ارْجِعِ الْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ يَنقَلِبْ إِلَيْكَ الْبَصَرُ خَاسِئًا وَهُوَ
حَسِيرٌ
Hausa
Sa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da
ganin wata naƙasa bã.
|
Ayah 67:5 الأية
وَلَقَدْ زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِمَصَابِيحَ وَجَعَلْنَاهَا رُجُومًا
لِّلشَّيَاطِينِ ۖ وَأَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابَ السَّعِيرِ
Hausa
Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga
shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr.
|
Ayah 67:6 الأية
وَلِلَّذِينَ كَفَرُوا بِرَبِّهِمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
Hausa
Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga
zamanta makõmarsu.
|
Ayah 67:7 الأية
إِذَا أُلْقُوا فِيهَا سَمِعُوا لَهَا شَهِيقًا وَهِيَ تَفُورُ
Hausa
Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa.
|
Ayah 67:8 الأية
تَكَادُ تَمَيَّزُ مِنَ الْغَيْظِ ۖ كُلَّمَا أُلْقِيَ فِيهَا فَوْجٌ سَأَلَهُمْ
خَزَنَتُهَا أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَذِيرٌ
Hausa
Tana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a
cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba?"
|
Ayah 67:9 الأية
قَالُوا بَلَىٰ قَدْ جَاءَنَا نَذِيرٌ فَكَذَّبْنَا وَقُلْنَا مَا نَزَّلَ اللَّهُ
مِن شَيْءٍ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا فِي ضَلَالٍ كَبِيرٍ
Hausa
Sai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce,
'Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.'"
|
Ayah 67:10 الأية
وَقَالُوا لَوْ كُنَّا نَسْمَعُ أَوْ نَعْقِلُ مَا كُنَّا فِي أَصْحَابِ السَّعِيرِ
Hausa
Kuma suka ce: "Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a
cikin 'yan sa'ĩr ba."
|
Ayah 67:11 الأية
فَاعْتَرَفُوا بِذَنبِهِمْ فَسُحْقًا لِّأَصْحَابِ السَّعِيرِ
Hausa
Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr!
|
Ayah 67:12 الأية
إِنَّ الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُم بِالْغَيْبِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ
كَبِيرٌ
Hausa
Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako
mai girma.
|
Ayah 67:13 الأية
وَأَسِرُّوا قَوْلَكُمْ أَوِ اجْهَرُوا بِهِ ۖ إِنَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
Hausa
Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin
da ke cikin ƙirãza.
|
Ayah 67:14 الأية
أَلَا يَعْلَمُ مَنْ خَلَقَ وَهُوَ اللَّطِيفُ الْخَبِيرُ
Hausa
Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa
ne, kuma Mai labartawa?
|
Ayah 67:15 الأية
هُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الْأَرْضَ ذَلُولًا فَامْشُوا فِي مَنَاكِبِهَا
وَكُلُوا مِن رِّزْقِهِ ۖ وَإِلَيْهِ النُّشُورُ
Hausa
Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma
ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake.
|
Ayah 67:16 الأية
أَأَمِنتُم مَّن فِي السَّمَاءِ أَن يَخْسِفَ بِكُمُ الْأَرْضَ فَإِذَا هِيَ
تَمُورُ
Hausa
Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku
ba, sai ga ta tana mai girgiza?
|
Ayah 67:17 الأية
أَمْ أَمِنتُم مَّن فِي السَّمَاءِ أَن يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا ۖ
فَسَتَعْلَمُونَ كَيْفَ نَذِيرِ
Hausa
Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To,
zã ku san yadda ( ãƙibar) gargaɗiNa take.
|
Ayah 67:18 الأية
وَلَقَدْ كَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
Hausa
Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗiNa ta
kasance?
|
Ayah 67:19 الأية
أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى الطَّيْرِ فَوْقَهُمْ صَافَّاتٍ وَيَقْبِضْنَ ۚ مَا
يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا الرَّحْمَٰنُ ۚ إِنَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ بَصِيرٌ
Hausa
Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa,
bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme.
|
Ayah 67:20 الأية
أَمَّنْ هَٰذَا الَّذِي هُوَ جُندٌ لَّكُمْ يَنصُرُكُم مِّن دُونِ الرَّحْمَٰنِ ۚ
إِنِ الْكَافِرُونَ إِلَّا فِي غُرُورٍ
Hausa
Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai
rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu.
|
Ayah 67:21 الأية
أَمَّنْ هَٰذَا الَّذِي يَرْزُقُكُمْ إِنْ أَمْسَكَ رِزْقَهُ ۚ بَل لَّجُّوا فِي
عُتُوٍّ وَنُفُورٍ
Hausa
Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikinSa? A'aha, sun yi
zurfi cikin girman kai da tãshin hankali.
|
Ayah 67:22 الأية
أَفَمَن يَمْشِي مُكِبًّا عَلَىٰ وَجْهِهِ أَهْدَىٰ أَمَّن يَمْشِي سَوِيًّا عَلَىٰ
صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Hausa
Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa
wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya?
|
Ayah 67:23 الأية
قُلْ هُوَ الَّذِي أَنشَأَكُمْ وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ
وَالْأَفْئِدَةَ ۖ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ
Hausa
Ka ce: "( Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da
tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!"
|
Ayah 67:24 الأية
قُلْ هُوَ الَّذِي ذَرَأَكُمْ فِي الْأَرْضِ وَإِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Hausa
Kuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gareShi ne ake tãshin ku."
|
Ayah 67:25 الأية
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Hausa
Kuma sunã cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu
gaskiya ne kũ?"
|
Ayah 67:26 الأية
قُلْ إِنَّمَا الْعِلْمُ عِندَ اللَّهِ وَإِنَّمَا أَنَا نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Hausa
Ka ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai
bayyana (gargaɗin)."
|
Ayah 67:27 الأية
فَلَمَّا رَأَوْهُ زُلْفَةً سِيئَتْ وُجُوهُ الَّذِينَ كَفَرُوا وَقِيلَ هَٰذَا
الَّذِي كُنتُم بِهِ تَدَّعُونَ
Hausa
To, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka
mũnana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa.
|
Ayah 67:28 الأية
قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَهْلَكَنِيَ اللَّهُ وَمَن مَّعِيَ أَوْ رَحِمَنَا فَمَن
يُجِيرُ الْكَافِرِينَ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ
Hausa
Ka ce musu "Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi
mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?"
|
Ayah 67:29 الأية
قُلْ هُوَ الرَّحْمَٰنُ آمَنَّا بِهِ وَعَلَيْهِ تَوَكَّلْنَا ۖ فَسَتَعْلَمُونَ
مَنْ هُوَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
Ka ce: "Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka
zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya."
|
Ayah 67:30 الأية
قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَصْبَحَ مَاؤُكُمْ غَوْرًا فَمَن يَأْتِيكُم بِمَاءٍ
مَّعِينٍ
Hausa
Ka ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku
da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?"
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|