Mutãnen Nũhu sun ƙaryata a gabãninsu, da ƙungiyõyin da suke a bãyansu, kuma
kõwace al'umma tã yi nufi game da Manzonsu, dõmin su kãmã shi. Kuma suka yi
jãyayya da ƙarya dõmin su gusar da gaskiya da ita. Sai Na kãmã su. To, yãya
azãbãTa take?
Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa
Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda
suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), "Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da
ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare
musu azãbar Jahĩm."
"Ya Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su a gidãjen Aljannar zama, wannan da Ka yi
musu wa'adi, sũ da wanda ya kyautatu daga ubanninsu da mãtan aurensu da
zurriyarsu. Lalle Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima."
"Kuma Ka tsare su daga mũnãnan ayyuka, kuma wanda Ka tsare shi daga mũnãnan
ayyuka a rãnarnan, to, lalle, Ka yi masa rahama kuma wancan shi ne babban rabo
mai girma."
Lalle waɗanda suka kãfirta, anã kiran su, "Haƙĩƙa, ƙin Allah (a gare ku) shĩ ne
mafi girma daga ƙinku ga kanku a lõkacin da ake kiran ku zuwa ga ĩmãni, sai kunã
ta kãfircẽwa."
Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Kã matar da mu sau biyu, kuma Kã rãyar da mu sau biyu,
sabõda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga
fita?"
Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirãyi Allah Shi kaɗai, sai ku kãfirta,
kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi ĩmãni. To, hukuncin fa, na Allah
Maɗaukaki, Mai girma ne.
Mai ɗaukaka darajõji (dõmin mũminai), Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi daga
al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar
gamuwa.
Rãnar da suke bayyanannu, bãbu wani abu daga gare su wanda yake iya bõyuwa ga
Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar (Sã'a) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke
mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu
wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu).
Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda
suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga
gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu.
Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah.
Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji
bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai
tsananin azãba.
Sa'an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: "Ku kashe
ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu." Kuma mugun
shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata.
Kuma Fir'auna ya ce: "Ku bar ni in kashe Mũsã, kuma shĩ, ya kirãyi Ubangijinsa.
Lalle ne nĩ, inã tsõron ya musanya addininku, kõ kuwa ya bayyana ɓarna a cikin
kasã."
Kuma wani namiji mũmini daga dangin Fir'auna, yanã bõye ĩmãninsa, ya ce: "Ashe,
za ku kashe mutum dõmin ya ce Ubangijina Allah ne, alhãli kuwa haƙĩƙa ya zo muku
da hujjõji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan yã kasance maƙaryaci ne, to,
ƙaryarsa na kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sãshen abin da yake yi
muku wa'adi zai sãme ku. Lalle ne Allah bã Ya shiryar da wanda yake mai barna,
mai yawan ƙarya."
"Yã kũ mutãnẽna! Kunã da mulki a yau, kuma kũ ne marinjãya a cikin kasã to wãne
ne zai taimake mu daga azãbar Allah idan ta zo mana?" Fir'auna ya ce: "Bã ni
nũnamuku kõme face abin da na gani, kuma ba ni shiryar da ku, sai ga hanyar
shiryuwa."
"A rãnar da zã ku jũya, kunã mãsu bãyar da bãya (gudãne) bã ku da wani mai tsaro
daga Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa."
"Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba
ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da
ya halaka kuka ce, 'Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa.' Kamar haka
Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka."
"Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba.
Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi
ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai
tĩlastãwa."
"¡õfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ
haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci." Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir'auna mũnãnan
aikinsakuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama
ba fãce yanã a cikin hasãra."
"Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma
wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne,
to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba."
"Kuna kira na zuwa ga in kãfirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da
abin da bãbu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni inã kiran ku zuwa ga
Mabuwãyi, Mai gãfara."
"Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, bã ya da wani kira a cikin
dũniya, kuma bã shi da shi a Lãhira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take,
kuma lalle mabarnata sũ ne 'yan wutã."
Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna (mabiya) su ce wa
waɗanda suka kangara (shugabanni), "Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to,
shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã?"
Suka ce: "Ashe, Manzanninku ba su jẽ muku da hujjõji bayyanannu ba?" Suka ce:
"Na'am, sun jẽ!" Suka ce: "To, ku rõƙa." Kuma rõƙon kãfirai bai zamo ba fãce a
cikin ɓata.
Sabõda haka, ka yi haƙuri, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nẽmi gãfara
ga zunubinka, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, maraice da kuma
wãyẽwar sãfiya.
Lalle waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, bã game da wani dalĩli wanda ya
jẽ musu ba, bãbu kõme a cikin kirãzansu, fãce girman kai, ba su zama mãsu isa ga
gũrinsu ba, sabõda haka ka nẽmi tsari daga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Mai
gani.
Kuma makãho da mai gani bã su daidaita kuma waɗanda suka yi ĩmãni suka, aikata
ayyukan ƙwarai da mai mũnanãwa bã su daidaita. Kaɗan ƙwarai, kuke yin tunãni.
Allah ne Wanda Ya sanya muku dare dõmin ku natsu a cikinsa, da rãna mai gãnarwa.
Lalle Allah, haƙĩƙa, Ma'abũcin falala ne a kan mutãne, kuma amma mafi yawan
mutãne bã su gõdẽwa.
Allah ne Ya sanya muku kasã tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya sũranta ku,
sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku,, kuma Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi.
Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana.
Shĩ ne Mai rai, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Sabõda haka ku kira Shi, kunã mãsu
tsarkake addini a gare Shi. Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
Ka ce: "Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a
lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in
sallama ga Ubangijin halittu."
Shĩ ne Wanda Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga maniyyi, sa'an nan daga
sãren jini, sa'an nan Ya fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan dõmin ku isa ga
cikar ƙarfinku sa'an nan dõmin ku kasance tsõfaffi, kuma daga cikinku, akwai
wanda ake karɓar ransa a gabãnin haka, kuma dõmin ku isa ga ajali ambatacce,
kuma dammãninku ko zã ku hankalta.
Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukunta wani al'amari,
to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance sai yana kasancewa (kamar yadda ake
bukatar sa.)
Sabõda haka ka yi haƙuri. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. To, kõ dai lalle Mu
nũna maka sãshen abin da Muka yi musu wa'adi da shi kõ kuwa lalle Mu karɓi
ranka, to, zuwa gare Mu ake mayar da su.
Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai
wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta
lãbãrinsa ba a gare ka. Bã ya yiwuwa ga wani Manzo ya jẽ da wata ãyar mu'ujiza
fãce da iznin Allah. Sa'an nan idan umurnin Allah ya jẽ, sai a yi hukunci da
gaskiya, mãsu ɓãtãwa sun yi hasara a can.
Ashe fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasã ba, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗanda ke
a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafi yawa daga gare su. Kuma sun fi tsananin
ƙarfi, da (yawan) gurãbun sanã'õ'i a cikin ƙasã. To, abin da suka kasance sunã
aikatãwa bai wadãtar da su ba.
A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki
da abin da ke wurinsu na ilmi kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi
ya wajaba a kansu.
To ĩmaninsu bai kasance yanã amfaninsu ba a lõkacin da suka ga azãbarMu. Hanyar
Allah wadda ta gabãta a cikin bãyinSa. Kuma kãfirai sun yi hasãra a can.