Yã san abin da yake shiga a cikin ƙasã da abin da yake fita daga gare ta, da
abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin
ƙai, Mai gãfara.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na
rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra bã
ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bã ta nĩsanta a cikin ƙasã, kuma
bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin Littãfi
bayyananne.
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi sunã ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga
Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yanã shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwãyi,
Gõdadde.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake
gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas,
kunã a cikin wata halitta sãbuwa.?"
Ashe fa, ba su yi dũbi ba zuwa ga abin da ke a gaba gare su da abin da ke a
bãyansu daga sama da ƙasã? idan Mun so, sai Mu shãfe ƙasã da su, kõ kuma Mu
kãyar da wani ɓaɓɓake daga sama a kansu. Lalle, a cikin wancan akwai ãyã ga
dukan bãwã mai maida al'amarinsa ga Allah.
Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda wata falala dagagare Mu. Yã duwatsu, ku
konkõma sautin tasbihi tãre da shi kuma da tsuntsãye. Kuma Muka tausasa masa
baƙin ƙarfe.
Kuma ga Sulaimãn, Mun hõre masa iska, tafiyarta ta safiya daidai da wata, kuma
ta maraice daidai da wata. Kuma Muka gudãnar masa da marmaron gaci, kuma daga
aljannu (Muka hõre masa) waɗanda ke aiki a gaba gare shi, da iznin Ubangijinsa.
Wanda ya karkata daga cikinsu, daga umurninMu, sai Mu ɗanɗana masa daga azãbar
sa'ĩr.
Sunã aikata masa abin da yake so, na masallatai da mutummutumai da akussa kamar
kududdufai, da tukwãne kafaffu. Ku aikata gõdiya, yã ɗiyan Dãwũda, kuma kaɗan ne
mai gõdiya daga bãyĩNa.
Sa'an nan a lõkacin da Muka hukunta mutuwa a kansa bãbu abin da ya ja
hankalinsu, a kan mutuwarsa, fãce dabbar ƙasa (gara) wadda take cin sandarsa. To
a lõkacin da ya fãɗi, sai aljannu suka bayyana (ga mutãne) cẽwa dã sun kasance
sun san gaibi, dã ba su zauna ba a cikin azãba mai wulãkantarwa.
Lalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu,
dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari
mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara."
Sai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka
musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan:
talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan.
Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin garũruwan da Muka Sanya albarka a
cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku
yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu."
Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka
zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce su
kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan
haƙuri, mai yawan gõdiya.
Kuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da
Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan
kõme, Mai tsaro ne.
Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã
su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa
kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa),kuma bã Shi da wani
mataimaki daga gare su.
"Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi.
Har a lõkacin da aka kuranye tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne
Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma,"
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba,
kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan
sama)." Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin
Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa
makangara (shũgabanni) "Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai."
Kuma maraunana suka ce wa makangara. "Ã'a, (ku tuna) mãkircin dare da na rãna a
lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan
tãrayya." Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka
sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu
sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya fãce mani'imtanta
(shũgabanni) sunce, "Lalle mũ, mãsu kãfirta ne da abin da aka aiko ku da shi."
Kuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da
ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙãmi fãce wanda, ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin
ƙwarai. To, waɗannan sunã da sakamakon ninkawa sabõda abin da suka aikata. Kuma
su amintattu ne a cikin bẽnãye.
Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa, kuma
Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai
musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa."
Sabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã
ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani
azabar wutã wadda "kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa."
Kuma idan an karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, sai su ce: "Wannan bai zama ba
fãce namiji ne yanã son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sunã
bauta wa." Kuma su ce: "Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya da aka ƙãga." Kuma
waɗanda suka kãfirta suka ce: ga gaskiya a lõkacin da ta je musu: "Wannan bã
kõme ba fãce sihiri ne bayyananne."
Kuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata ,alhãli kuwa ba su kai
ushurin-ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata ManzanniNa! To, yãya
musũNa (ga maƙaryata) ya kasance?
Ka ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dõmin Allah,
bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunãni, bãbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ
bai zama ba fãce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azãba mai tsanani.
Ka ce: "Idan na ɓace, to, inã ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu,
to, sabõda abin da Ubangijina Yake yõwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai
ji ne, Makusanci."
Kuma an shãmakance a tsakãninsu da tsakãnin abin da suke marmari, kamar yadda
aka aikata da irin ƙungiyõyinsu a gabãninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka
mai sanya kõkanto.