« Prev

34. Surah Saba' سورة سبأ

Next »First Ayah   1   الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَلَهُ الْحَمْدُ فِي الْآخِرَةِ ۚ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْخَبِيرُ
Hausa
 
Gődiya ta tabbata ga Allah, wanda Yake abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasă Năsa ne, kuma shĩ ne Mai hikima, Mai labartawa.

Ayah   34:2   الأية
يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا ۚ وَهُوَ الرَّحِيمُ الْغَفُورُ
Hausa
 
Yă san abin da yake shiga a cikin ƙasă da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin ƙai, Mai găfara.

Ayah   34:3   الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَا تَأْتِينَا السَّاعَةُ ۖ قُلْ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتَأْتِيَنَّكُمْ عَالِمِ الْغَيْبِ ۖ لَا يَعْزُبُ عَنْهُ مِثْقَالُ ذَرَّةٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ وَلَا أَصْغَرُ مِن ذَٰلِكَ وَلَا أَكْبَرُ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta suka ce: "Să'a bă ză ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, ză ta ző muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra bă ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bă ta nĩsanta a cikin ƙasă, kuma băbu mafi ƙaranci daga wancan kuma băbu mafi girma făce yană a cikin Littăfi bayyananne.

Ayah   34:4   الأية
لِّيَجْزِيَ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ۚ أُولَٰئِكَ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
Hausa
 
Dőmin Ya săkă wa waɗanda suka yi ĩmăni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata găfara da wani arziki mai karimci.

Ayah   34:5   الأية
وَالَّذِينَ سَعَوْا فِي آيَاتِنَا مُعَاجِزِينَ أُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مِّن رِّجْزٍ أَلِيمٌ
Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi măkirci ga ăyőyinMu, sună măsu gajiyarwa, waɗannan sună da wata azăba daga azăba mai raɗaɗi.

Ayah   34:6   الأية
وَيَرَى الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ الَّذِي أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ هُوَ الْحَقَّ وَيَهْدِي إِلَىٰ صِرَاطِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ
Hausa
 
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi sună ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yană shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwăyi, Gődadde.

Ayah   34:7   الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا هَلْ نَدُلُّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ يُنَبِّئُكُمْ إِذَا مُزِّقْتُمْ كُلَّ مُمَزَّقٍ إِنَّكُمْ لَفِي خَلْقٍ جَدِيدٍ
Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta suka ce: "Shin ză mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsăge ku, kőwace irin tsattsăgẽwa, lalle kũ, tabbas, kună a cikin wata halitta săbuwa.?"

Ayah   34:8   الأية
أَفْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا أَم بِهِ جِنَّةٌ ۗ بَلِ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ فِي الْعَذَابِ وَالضَّلَالِ الْبَعِيدِ
Hausa
 
"Ya ƙăga ƙarya ga Allah ne kő kuwa akwai wata hauka a gare shi?" Ă'a, waɗanda ba su yi ĩmăni da Lăhira ba, sună a cikin azăba da ɓăta mai nĩsa.

Ayah   34:9   الأية
أَفَلَمْ يَرَوْا إِلَىٰ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُم مِّنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۚ إِن نَّشَأْ نَخْسِفْ بِهِمُ الْأَرْضَ أَوْ نُسْقِطْ عَلَيْهِمْ كِسَفًا مِّنَ السَّمَاءِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ
Hausa
 
Ashe fa, ba su yi dũbi ba zuwa ga abin da ke a gaba gare su da abin da ke a băyansu daga sama da ƙasă? idan Mun so, sai Mu shăfe ƙasă da su, kő kuma Mu kăyar da wani ɓaɓɓake daga sama a kansu. Lalle, a cikin wancan akwai ăyă ga dukan băwă mai maida al'amarinsa ga Allah.

Ayah   34:10   الأية
وَلَقَدْ آتَيْنَا دَاوُودَ مِنَّا فَضْلًا ۖ يَا جِبَالُ أَوِّبِي مَعَهُ وَالطَّيْرَ ۖ وَأَلَنَّا لَهُ الْحَدِيدَ
Hausa
 
Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun bai wa Dăwũda wata falala dagagare Mu. Yă duwatsu, ku konkőma sautin tasbihi tăre da shi kuma da tsuntsăye. Kuma Muka tausasa masa baƙin ƙarfe.

Ayah   34:11   الأية
أَنِ اعْمَلْ سَابِغَاتٍ وَقَدِّرْ فِي السَّرْدِ ۖ وَاعْمَلُوا صَالِحًا ۖ إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ
Hausa
 
Ka aikata sulkuna kuma ka ƙaddara lissăfi ga tsărawa, kuma ka aikata aikin ƙwarai. Lalle NĩMai gani ne ga abin da kuke aikatăwa.

Ayah   34:12   الأية
وَلِسُلَيْمَانَ الرِّيحَ غُدُوُّهَا شَهْرٌ وَرَوَاحُهَا شَهْرٌ ۖ وَأَسَلْنَا لَهُ عَيْنَ الْقِطْرِ ۖ وَمِنَ الْجِنِّ مَن يَعْمَلُ بَيْنَ يَدَيْهِ بِإِذْنِ رَبِّهِ ۖ وَمَن يَزِغْ مِنْهُمْ عَنْ أَمْرِنَا نُذِقْهُ مِنْ عَذَابِ السَّعِيرِ
Hausa
 
Kuma ga Sulaimăn, Mun hőre masa iska, tafiyarta ta safiya daidai da wata, kuma ta maraice daidai da wata. Kuma Muka gudănar masa da marmaron gaci, kuma daga aljannu (Muka hőre masa) waɗanda ke aiki a gaba gare shi, da iznin Ubangijinsa. Wanda ya karkata daga cikinsu, daga umurninMu, sai Mu ɗanɗana masa daga azăbar sa'ĩr.

Ayah   34:13   الأية
يَعْمَلُونَ لَهُ مَا يَشَاءُ مِن مَّحَارِيبَ وَتَمَاثِيلَ وَجِفَانٍ كَالْجَوَابِ وَقُدُورٍ رَّاسِيَاتٍ ۚ اعْمَلُوا آلَ دَاوُودَ شُكْرًا ۚ وَقَلِيلٌ مِّنْ عِبَادِيَ الشَّكُورُ
Hausa
 
Sună aikata masa abin da yake so, na masallatai da mutummutumai da akussa kamar kududdufai, da tukwăne kafaffu. Ku aikata gődiya, yă ɗiyan Dăwũda, kuma kaɗan ne mai gődiya daga băyĩNa.

Ayah   34:14   الأية
فَلَمَّا قَضَيْنَا عَلَيْهِ الْمَوْتَ مَا دَلَّهُمْ عَلَىٰ مَوْتِهِ إِلَّا دَابَّةُ الْأَرْضِ تَأْكُلُ مِنسَأَتَهُ ۖ فَلَمَّا خَرَّ تَبَيَّنَتِ الْجِنُّ أَن لَّوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ الْغَيْبَ مَا لَبِثُوا فِي الْعَذَابِ الْمُهِينِ
Hausa
 
Sa'an nan a lőkacin da Muka hukunta mutuwa a kansa băbu abin da ya ja hankalinsu, a kan mutuwarsa, făce dabbar ƙasa (gara) wadda take cin sandarsa. To a lőkacin da ya făɗi, sai aljannu suka bayyana (ga mutăne) cẽwa dă sun kasance sun san gaibi, dă ba su zauna ba a cikin azăba mai wulăkantarwa.

Ayah   34:15   الأية
لَقَدْ كَانَ لِسَبَإٍ فِي مَسْكَنِهِمْ آيَةٌ ۖ جَنَّتَانِ عَن يَمِينٍ وَشِمَالٍ ۖ كُلُوا مِن رِّزْقِ رَبِّكُمْ وَاشْكُرُوا لَهُ ۚ بَلْدَةٌ طَيِّبَةٌ وَرَبٌّ غَفُورٌ
Hausa
 
Lalle, haƙĩƙa, akwai ăyă ga saba'ăwa a cikin mazauninsu: gőnakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gődiya gare shi. Gari mai dăɗin zama, da Ubangiji Mai găfara."

Ayah   34:16   الأية
فَأَعْرَضُوا فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ سَيْلَ الْعَرِمِ وَبَدَّلْنَاهُم بِجَنَّتَيْهِمْ جَنَّتَيْنِ ذَوَاتَيْ أُكُلٍ خَمْطٍ وَأَثْلٍ وَشَيْءٍ مِّن سِدْرٍ قَلِيلٍ
Hausa
 
Sai suka bijire sabőda haka Muka saki Mălălin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gőnakinsu biyu da waɗansu gőnaki biyu măsu 'ya'yan ităce kaɗan: talăkiya da gőriba da wani abu na magarya kaɗan.

Ayah   34:17   الأية
ذَٰلِكَ جَزَيْنَاهُم بِمَا كَفَرُوا ۖ وَهَلْ نُجَازِي إِلَّا الْكَفُورَ
Hausa
 
Wancan, da shi Muka yi musu sakamako sabőda kăfircinsu. Kuma lalle, bă Mu yi wa kőwa irin wannan sakamako, făce kafirai.

Ayah   34:18   الأية
وَجَعَلْنَا بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ الْقُرَى الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا قُرًى ظَاهِرَةً وَقَدَّرْنَا فِيهَا السَّيْرَ ۖ سِيرُوا فِيهَا لَيَالِيَ وَأَيَّامًا آمِنِينَ
Hausa
 
Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakănin garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa măsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rănaiku, kună amintattu."

Ayah   34:19   الأية
فَقَالُوا رَبَّنَا بَاعِدْ بَيْنَ أَسْفَارِنَا وَظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ فَجَعَلْنَاهُمْ أَحَادِيثَ وَمَزَّقْنَاهُمْ كُلَّ مُمَزَّقٍ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ
Hausa
 
Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakănin tafiyőyinmu," kuma suka zălunci kansu, sabőda haka Muka sanya su lăbăran hĩra kuma Muka kekkẽce su kőwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ăyőyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gődiya.

Ayah   34:20   الأية
وَلَقَدْ صَدَّقَ عَلَيْهِمْ إِبْلِيسُ ظَنَّهُ فَاتَّبَعُوهُ إِلَّا فَرِيقًا مِّنَ الْمُؤْمِنِينَ
Hausa
 
Kuma lalle, haƙĩƙa, Iblĩs ya gaskata zatonsa a kansu, sai suka bi shi făce wani ɓangare na mũminai.

Ayah   34:21   الأية
وَمَا كَانَ لَهُ عَلَيْهِم مِّن سُلْطَانٍ إِلَّا لِنَعْلَمَ مَن يُؤْمِنُ بِالْآخِرَةِ مِمَّنْ هُوَ مِنْهَا فِي شَكٍّ ۗ وَرَبُّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ حَفِيظٌ
Hausa
 
Kuma bă ya da wani dalĩli a kansu făce dai dőmin Mu san wanda yake yin ĩmăni da Lăhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kőme, Mai tsaro ne.

Ayah   34:22   الأية
قُلِ ادْعُوا الَّذِينَ زَعَمْتُم مِّن دُونِ اللَّهِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ وَمَا لَهُمْ فِيهِمَا مِن شِرْكٍ وَمَا لَهُ مِنْهُم مِّن ظَهِيرٍ
Hausa
 
Ka ce: "Ku kirăyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautăwa ne) baicin Allah, bă su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bă su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bă su da wani rabon tărẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa),kuma bă Shi da wani mataimaki daga gare su.

Ayah   34:23   الأية
وَلَا تَنفَعُ الشَّفَاعَةُ عِندَهُ إِلَّا لِمَنْ أَذِنَ لَهُ ۚ حَتَّىٰ إِذَا فُزِّعَ عَن قُلُوبِهِمْ قَالُوا مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ ۖ قَالُوا الْحَقَّ ۖ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ
Hausa
 
"Kuma wani cẽto bă ya amfăni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lőkacin da aka kuranye tsőro daga zukătansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma,"

Ayah   34:24   الأية
قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ قُلِ اللَّهُ ۖ وَإِنَّا أَوْ إِيَّاكُمْ لَعَلَىٰ هُدًى أَوْ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
Ka ce: "Wăne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kő ku, wani yană a kan shiriya, kő yana a cikin ɓata bayyananniya."

Ayah   34:25   الأية
قُل لَّا تُسْأَلُونَ عَمَّا أَجْرَمْنَا وَلَا نُسْأَلُ عَمَّا تَعْمَلُونَ
Hausa
 
Ka ce: "Bă ză a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bă ză a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba."

Ayah   34:26   الأية
قُلْ يَجْمَعُ بَيْنَنَا رَبُّنَا ثُمَّ يَفْتَحُ بَيْنَنَا بِالْحَقِّ وَهُوَ الْفَتَّاحُ الْعَلِيمُ
Hausa
 
Ka ce: "Ubangijinmu zai tăra tsakăninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani."

Ayah   34:27   الأية
قُلْ أَرُونِيَ الَّذِينَ أَلْحَقْتُم بِهِ شُرَكَاءَ ۖ كَلَّا ۚ بَلْ هُوَ اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Hausa
 
Ka ce: "Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abőkan tărayya. Ă'a, Shĩ ne Allah, Mabuwăyi, Mai hikima."

Ayah   34:28   الأية
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا كَافَّةً لِّلنَّاسِ بَشِيرًا وَنَذِيرًا وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Hausa
 
Kuma ba Mu aika ka ba făce zuwa ga mutăne gabă ɗaya, kană mai băyar da bushăra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutăne ba su sani ba.

Ayah   34:29   الأية
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Hausa
 
Sună cẽwa, "Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance măsu gaskiya?"

Ayah   34:30   الأية
قُل لَّكُم مِّيعَادُ يَوْمٍ لَّا تَسْتَأْخِرُونَ عَنْهُ سَاعَةً وَلَا تَسْتَقْدِمُونَ
Hausa
 
Ka ce: "Kună da mi'ădin wani yini wanda bă ku jinkirta daga gare shi kő da sa'a ɗaya, kuma bă ku gabăta."

Ayah   34:31   الأية
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَن نُّؤْمِنَ بِهَٰذَا الْقُرْآنِ وَلَا بِالَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ ۗ وَلَوْ تَرَىٰ إِذِ الظَّالِمُونَ مَوْقُوفُونَ عِندَ رَبِّهِمْ يَرْجِعُ بَعْضُهُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ الْقَوْلَ يَقُولُ الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا لَوْلَا أَنتُمْ لَكُنَّا مُؤْمِنِينَ
Hausa
 
Kuma waɗanda suka kăfirta suka ce: "Bă ză mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ăni ba, kuma bă ză mu yi ĩmani da abin da yakea gabăninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma dă kă gani a lőkacin da azzălumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa săshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) "Ba dőminku ba, lalle, dă mun kasance mũminai."

Ayah   34:32   الأية
قَالَ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا لِلَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا أَنَحْنُ صَدَدْنَاكُمْ عَنِ الْهُدَىٰ بَعْدَ إِذْ جَاءَكُم ۖ بَلْ كُنتُم مُّجْرِمِينَ
Hausa
 
Makangara suka ce wa maraunana, "Ashe, mũ ne muka kange ku daga shiriya a băyan ya zo muku? Ă,a' kun dai kasance măsu laifi."

Ayah   34:33   الأية
وَقَالَ الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا بَلْ مَكْرُ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ إِذْ تَأْمُرُونَنَا أَن نَّكْفُرَ بِاللَّهِ وَنَجْعَلَ لَهُ أَندَادًا ۚ وَأَسَرُّوا النَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُا الْعَذَابَ وَجَعَلْنَا الْأَغْلَالَ فِي أَعْنَاقِ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ هَلْ يُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Hausa
 
Kuma maraunana suka ce wa makangara. "Ă'a, (ku tuna) măkircin dare da na răna a lőkacin da kuke umurnin mu da mu kăfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abőkan tărayya." Kuma suka assirtar da nadăma a lőkacin da suka ga azăba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyőyin waɗanda suka kăfirta. Lalle, bă ză a yi musu sakamako ba făce da abin da suka kasance sună aikatăwa.

Ayah   34:34   الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا فِي قَرْيَةٍ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَا إِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُم بِهِ كَافِرُونَ
Hausa
 
Kuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya făce mani'imtanta (shũgabanni) sunce, "Lalle mũ, măsu kăfirta ne da abin da aka aiko ku da shi."

Ayah   34:35   الأية
وَقَالُوا نَحْنُ أَكْثَرُ أَمْوَالًا وَأَوْلَادًا وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ
Hausa
 
Kuma suka ce: "Mũ ne mafiya yawa ga dũkiya da ɗiya, kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azăba ba."

Ayah   34:36   الأية
قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Hausa
 
Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yană shimfiɗa arziki ga wanda Ya so, kuma Yană ƙuntatăwa, kuma amma mafi yawan mutăne ba su sani ba."

Ayah   34:37   الأية
وَمَا أَمْوَالُكُمْ وَلَا أَوْلَادُكُم بِالَّتِي تُقَرِّبُكُمْ عِندَنَا زُلْفَىٰ إِلَّا مَنْ آمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ لَهُمْ جَزَاءُ الضِّعْفِ بِمَا عَمِلُوا وَهُمْ فِي الْغُرُفَاتِ آمِنُونَ
Hausa
 
Kuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙămi făce wanda, ya yi ĩmăni kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan sună da sakamakon ninkawa sabőda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin bẽnăye.

Ayah   34:38   الأية
وَالَّذِينَ يَسْعَوْنَ فِي آيَاتِنَا مُعَاجِزِينَ أُولَٰئِكَ فِي الْعَذَابِ مُحْضَرُونَ
Hausa
 
Kuma waɗanda suke măkirci a cikin ăyőyinMu, sună nẽman gajiyarwa, waɗannan abin halartăwa ne a cikin azăba.

Ayah   34:39   الأية
قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَيَقْدِرُ لَهُ ۚ وَمَا أَنفَقْتُم مِّن شَيْءٍ فَهُوَ يُخْلِفُهُ ۖ وَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Hausa
 
Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yană shimfida arziki ga wanda Ya so daga băyinSa, kuma Yană ƙuntatăwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin măsu azurtawa."

Ayah   34:40   الأية
وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ جَمِيعًا ثُمَّ يَقُولُ لِلْمَلَائِكَةِ أَهَٰؤُلَاءِ إِيَّاكُمْ كَانُوا يَعْبُدُونَ
Hausa
 
Kuma rănar da Allah Ya ke tăra su gabă ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Mală'iku, "Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sună bauta wa?"

Ayah   34:41   الأية
قَالُوا سُبْحَانَكَ أَنتَ وَلِيُّنَا مِن دُونِهِم ۖ بَلْ كَانُوا يَعْبُدُونَ الْجِنَّ ۖ أَكْثَرُهُم بِهِم مُّؤْمِنُونَ
Hausa
 
Sukace: "Tsarki ya tabbata a gare Ka. Kai ne Majiɓincinmu, bă su ba. Ă'a,sun kasance sună bauta wa aljannu. Mafi yawansu, da sũ suka yi ĩmani."

Ayah   34:42   الأية
فَالْيَوْمَ لَا يَمْلِكُ بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ نَّفْعًا وَلَا ضَرًّا وَنَقُولُ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا ذُوقُوا عَذَابَ النَّارِ الَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
Hausa
 
Sabőda haka, a yau săshenku bă ya mallakar wani amfăni ga wani săshen, kuma bă ya mallakar wata cũta, kuma Mună cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wută wadda "kuka kasance game da ita, kună ƙaryatăwa."

Ayah   34:43   الأية
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ قَالُوا مَا هَٰذَا إِلَّا رَجُلٌ يُرِيدُ أَن يَصُدَّكُمْ عَمَّا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُكُمْ وَقَالُوا مَا هَٰذَا إِلَّا إِفْكٌ مُّفْتَرًى ۚ وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُمْ إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ
Hausa
 
Kuma idan an karanta ăyőyinMu bayyanannu a kansu, sai su ce: "Wannan bai zama ba făce namiji ne yană son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sună bauta wa." Kuma su ce: "Wannan bai zama ba făce ƙiren ƙarya da aka ƙăga." Kuma waɗanda suka kăfirta suka ce: ga gaskiya a lőkacin da ta je musu: "Wannan bă kőme ba făce sihiri ne bayyananne."

Ayah   34:44   الأية
وَمَا آتَيْنَاهُم مِّن كُتُبٍ يَدْرُسُونَهَا ۖ وَمَا أَرْسَلْنَا إِلَيْهِمْ قَبْلَكَ مِن نَّذِيرٍ
Hausa
 
Kuma ba Mu bă su waɗansu littattafai ba waɗanda suke karătun su, kuma ba Mu aika wani mai gargaɗi ba zuwa gare su a gabăninka!

Ayah   34:45   الأية
وَكَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ وَمَا بَلَغُوا مِعْشَارَ مَا آتَيْنَاهُمْ فَكَذَّبُوا رُسُلِي ۖ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
Hausa
 
Kuma waɗanda suke a gabăninsu, sun ƙaryata ,alhăli kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka bă su ba, sai suka ƙaryata ManzanniNa! To, yăya musũNa (ga maƙaryata) ya kasance?

Ayah   34:46   الأية
قُلْ إِنَّمَا أَعِظُكُم بِوَاحِدَةٍ ۖ أَن تَقُومُوا لِلَّهِ مَثْنَىٰ وَفُرَادَىٰ ثُمَّ تَتَفَكَّرُوا ۚ مَا بِصَاحِبِكُم مِّن جِنَّةٍ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا نَذِيرٌ لَّكُم بَيْنَ يَدَيْ عَذَابٍ شَدِيدٍ
Hausa
 
Ka ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dőmin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunăni, băbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ bai zama ba făce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azăba mai tsanani.

Ayah   34:47   الأية
قُلْ مَا سَأَلْتُكُم مِّنْ أَجْرٍ فَهُوَ لَكُمْ ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى اللَّهِ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ
Hausa
 
Ka ce: "Abin da na rőƙe ku na wani sakamako, to, amfăninsa năku ne. Ijărata ba ta zama ba făce daga Allah, kuma shi Mahalarci ne a kan dukan kőme."

Ayah   34:48   الأية
قُلْ إِنَّ رَبِّي يَقْذِفُ بِالْحَقِّ عَلَّامُ الْغُيُوبِ
Hausa
 
Ka ce: "Lalle Ubangijina Yană jẽfa gaskiya.(Shi) Masanin abũbuwan fake ne."

Ayah   34:49   الأية
قُلْ جَاءَ الْحَقُّ وَمَا يُبْدِئُ الْبَاطِلُ وَمَا يُعِيدُ
Hausa
 
Ka ce: "Gaskiya ta zo, kuma ƙarya bă ta iya fara (kome) kuma bă ta iya mayarwa."

Ayah   34:50   الأية
قُلْ إِن ضَلَلْتُ فَإِنَّمَا أَضِلُّ عَلَىٰ نَفْسِي ۖ وَإِنِ اهْتَدَيْتُ فَبِمَا يُوحِي إِلَيَّ رَبِّي ۚ إِنَّهُ سَمِيعٌ قَرِيبٌ
Hausa
 
Ka ce: "Idan na ɓace, to, ină ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, sabőda abin da Ubangijina Yake yőwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai ji ne, Makusanci."

Ayah   34:51   الأية
وَلَوْ تَرَىٰ إِذْ فَزِعُوا فَلَا فَوْتَ وَأُخِذُوا مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ
Hausa
 
Kuma dă kă gani, a lőkacin da suka firgita, to, băbu kuɓuta, kuma aka kăma su daga wuri makusanci.

Ayah   34:52   الأية
وَقَالُوا آمَنَّا بِهِ وَأَنَّىٰ لَهُمُ التَّنَاوُشُ مِن مَّكَانٍ بَعِيدٍ
Hausa
 
Kuma suka ce: "Mun yi ĩmăni da Shi." To ină ză su sămu kămăwa daga wuri mai nisa?

Ayah   34:53   الأية
وَقَدْ كَفَرُوا بِهِ مِن قَبْلُ ۖ وَيَقْذِفُونَ بِالْغَيْبِ مِن مَّكَانٍ بَعِيدٍ
Hausa
 
Kuma lalle sun kăfirta da Shi a gabănin haka, kuma sună jĩfa da jăhilci daga wuri mai nĩsa.

Ayah   34:54   الأية
وَحِيلَ بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ مَا يَشْتَهُونَ كَمَا فُعِلَ بِأَشْيَاعِهِم مِّن قَبْلُ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا فِي شَكٍّ مُّرِيبٍ
Hausa
 
Kuma an shămakance a tsakăninsu da tsakănin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyőyinsu a gabăninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka mai sanya kőkanto. 
 


© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us