« Prev

4. Surah An-Nisâ' سورة النساء

Next »First Ayah   1   الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَاحِدَةٍ وَخَلَقَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالًا كَثِيرًا وَنِسَاءً ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي تَسَاءَلُونَ بِهِ وَالْأَرْحَامَ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَيْكُمْ رَقِيبًا
Hausa
 
Ya ku mutăne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza măsu yawa da mătă. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rőƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta . Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.

Ayah   4:2   الأية
وَآتُوا الْيَتَامَىٰ أَمْوَالَهُمْ ۖ وَلَا تَتَبَدَّلُوا الْخَبِيثَ بِالطَّيِّبِ ۖ وَلَا تَأْكُلُوا أَمْوَالَهُمْ إِلَىٰ أَمْوَالِكُمْ ۚ إِنَّهُ كَانَ حُوبًا كَبِيرًا
Hausa
 
Kuma ku bai wa marăyu dũkiyőyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau. Kuma kada ku ci dũkiyőyinsu zuwa ga dũkiyőyinku. Lalle shi, yă kasance zunubi ne mai girma.

Ayah   4:3   الأية
وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَىٰ فَانكِحُوا مَا طَابَ لَكُم مِّنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا
Hausa
 
Kuma idan kun ji tsőron bă ză ku yi ădalci ba a cikin marăyu, to, (akwai yadda ză a yi) ku auri abin da ya yi muku dăɗi daga mătă; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsőron bă ză ku yi ădalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.

Ayah   4:4   الأية
وَآتُوا النِّسَاءَ صَدُقَاتِهِنَّ نِحْلَةً ۚ فَإِن طِبْنَ لَكُمْ عَن شَيْءٍ مِّنْهُ نَفْسًا فَكُلُوهُ هَنِيئًا مَّرِيئًا
Hausa
 
Kuma ku bai wa mătă sadăkőkĩnsu da sauƙin băyarwa. Sa'an nan idan suka yăfe muku wani abu daga gare shi, da dăɗin rai, to, ku ci shi da jin dăɗi da sauƙin haɗiya.

Ayah   4:5   الأية
وَلَا تُؤْتُوا السُّفَهَاءَ أَمْوَالَكُمُ الَّتِي جَعَلَ اللَّهُ لَكُمْ قِيَامًا وَارْزُقُوهُمْ فِيهَا وَاكْسُوهُمْ وَقُولُوا لَهُمْ قَوْلًا مَّعْرُوفًا
Hausa
 
Kada ku bai wa wăwăye dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kună măsu tsayuwa (ga gyăranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufătar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.

Ayah   4:6   الأية
وَابْتَلُوا الْيَتَامَىٰ حَتَّىٰ إِذَا بَلَغُوا النِّكَاحَ فَإِنْ آنَسْتُم مِّنْهُمْ رُشْدًا فَادْفَعُوا إِلَيْهِمْ أَمْوَالَهُمْ ۖ وَلَا تَأْكُلُوهَا إِسْرَافًا وَبِدَارًا أَن يَكْبَرُوا ۚ وَمَن كَانَ غَنِيًّا فَلْيَسْتَعْفِفْ ۖ وَمَن كَانَ فَقِيرًا فَلْيَأْكُلْ بِالْمَعْرُوفِ ۚ فَإِذَا دَفَعْتُمْ إِلَيْهِمْ أَمْوَالَهُمْ فَأَشْهِدُوا عَلَيْهِمْ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ حَسِيبًا
Hausa
 
Kuma ku jarraba marăyu, har a lőkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyőyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma da gaggawa kăfin su girma. Kuma wanda yake wadătacce, to, ya kăma kănsa, kuma wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu dũkiyőyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike.

Ayah   4:7   الأية
لِّلرِّجَالِ نَصِيبٌ مِّمَّا تَرَكَ الْوَالِدَانِ وَالْأَقْرَبُونَ وَلِلنِّسَاءِ نَصِيبٌ مِّمَّا تَرَكَ الْوَالِدَانِ وَالْأَقْرَبُونَ مِمَّا قَلَّ مِنْهُ أَوْ كَثُرَ ۚ نَصِيبًا مَّفْرُوضًا
Hausa
 
Maza suna da rabo daga abin da iyăye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mătă suna da rabo daga abin da iyăye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kő kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.

Ayah   4:8   الأية
وَإِذَا حَضَرَ الْقِسْمَةَ أُولُو الْقُرْبَىٰ وَالْيَتَامَىٰ وَالْمَسَاكِينُ فَارْزُقُوهُم مِّنْهُ وَقُولُوا لَهُمْ قَوْلًا مَّعْرُوفًا
Hausa
 
Kuma idan ma'abũta zumunta da marăyu da matalauta suka halarci rabon, to, ku azurta su daga gare shi, kuma ku faɗa musu magana sananniya ta alhẽri.

Ayah   4:9   الأية
وَلْيَخْشَ الَّذِينَ لَوْ تَرَكُوا مِنْ خَلْفِهِمْ ذُرِّيَّةً ضِعَافًا خَافُوا عَلَيْهِمْ فَلْيَتَّقُوا اللَّهَ وَلْيَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke dă sun bar zuriyya măsu rauni a băyansu, ză su ji tsőro a kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana madaidaiciya.

Ayah   4:10   الأية
إِنَّ الَّذِينَ يَأْكُلُونَ أَمْوَالَ الْيَتَامَىٰ ظُلْمًا إِنَّمَا يَأْكُلُونَ فِي بُطُونِهِمْ نَارًا ۖ وَسَيَصْلَوْنَ سَعِيرًا
Hausa
 
Lalle ne, waɗanda suke cĩn dũkiyar marăyu da zălunci, to, wuta kawai suke ci a cikin cikkunansu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani.

Ayah   4:11   الأية
يُوصِيكُمُ اللَّهُ فِي أَوْلَادِكُمْ ۖ لِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنثَيَيْنِ ۚ فَإِن كُنَّ نِسَاءً فَوْقَ اثْنَتَيْنِ فَلَهُنَّ ثُلُثَا مَا تَرَكَ ۖ وَإِن كَانَتْ وَاحِدَةً فَلَهَا النِّصْفُ ۚ وَلِأَبَوَيْهِ لِكُلِّ وَاحِدٍ مِّنْهُمَا السُّدُسُ مِمَّا تَرَكَ إِن كَانَ لَهُ وَلَدٌ ۚ فَإِن لَّمْ يَكُن لَّهُ وَلَدٌ وَوَرِثَهُ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ الثُّلُثُ ۚ فَإِن كَانَ لَهُ إِخْوَةٌ فَلِأُمِّهِ السُّدُسُ ۚ مِن بَعْدِ وَصِيَّةٍ يُوصِي بِهَا أَوْ دَيْنٍ ۗ آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ لَا تَدْرُونَ أَيُّهُمْ أَقْرَبُ لَكُمْ نَفْعًا ۚ فَرِيضَةً مِّنَ اللَّهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا
Hausa
 
Allah Yană yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yană da rabon mătă biyu. Idan sun kasance mătă ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma iyăyensa biyu kőwane ɗaya daga cikinsu yană da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi ba, kuma iyăyensa ne (kawai) suka găje shi, to, uwa tană da sulusi (ɗaya daga cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kő kuwa băshi. Ubanninku da 'yă'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yă kasance Masani Mai hikima.

Ayah   4:12   الأية
وَلَكُمْ نِصْفُ مَا تَرَكَ أَزْوَاجُكُمْ إِن لَّمْ يَكُن لَّهُنَّ وَلَدٌ ۚ فَإِن كَانَ لَهُنَّ وَلَدٌ فَلَكُمُ الرُّبُعُ مِمَّا تَرَكْنَ ۚ مِن بَعْدِ وَصِيَّةٍ يُوصِينَ بِهَا أَوْ دَيْنٍ ۚ وَلَهُنَّ الرُّبُعُ مِمَّا تَرَكْتُمْ إِن لَّمْ يَكُن لَّكُمْ وَلَدٌ ۚ فَإِن كَانَ لَكُمْ وَلَدٌ فَلَهُنَّ الثُّمُنُ مِمَّا تَرَكْتُم ۚ مِّن بَعْدِ وَصِيَّةٍ تُوصُونَ بِهَا أَوْ دَيْنٍ ۗ وَإِن كَانَ رَجُلٌ يُورَثُ كَلَالَةً أَوِ امْرَأَةٌ وَلَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ وَاحِدٍ مِّنْهُمَا السُّدُسُ ۚ فَإِن كَانُوا أَكْثَرَ مِن ذَٰلِكَ فَهُمْ شُرَكَاءُ فِي الثُّلُثِ ۚ مِن بَعْدِ وَصِيَّةٍ يُوصَىٰ بِهَا أَوْ دَيْنٍ غَيْرَ مُضَارٍّ ۚ وَصِيَّةً مِّنَ اللَّهِ ۗ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَلِيمٌ
Hausa
 
Kuma kună da rabin abin da mătanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kună da rubu'i (ɗaya daga cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga băyan wasiyya wadda suka yi kő kuma băshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sună da sumuni (ɗaya daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga băyan wasiyya wadda kuka yi kő kuwa băshi. Idan wani namiji ya kasance ana gădon sa bisa kalăla, ko kuwa wata mace alhăli kuwa yana da ɗan'uwa kő 'yar'uwa to, kőwane ɗaya daga cikinsu yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa daga wannan, to, sũ abőkan tărayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga băyan wasiyya wadda aka yi kő kuma băshi. Bă da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri.

Ayah   4:13   الأية
تِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ ۚ وَمَن يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ يُدْخِلْهُ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ وَذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Hausa
 
Waɗancan iyăkőkin Allah ne. Wanda ya yi ɗă'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi gidăjen Aljanna (waɗanda) ɗőramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba.

Ayah   4:14   الأية
وَمَن يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُ يُدْخِلْهُ نَارًا خَالِدًا فِيهَا وَلَهُ عَذَابٌ مُّهِينٌ
Hausa
 
Kuma wanda ya săɓă wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyăkőkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azăba mai walăkantarwa.

Ayah   4:15   الأية
وَاللَّاتِي يَأْتِينَ الْفَاحِشَةَ مِن نِّسَائِكُمْ فَاسْتَشْهِدُوا عَلَيْهِنَّ أَرْبَعَةً مِّنكُمْ ۖ فَإِن شَهِدُوا فَأَمْسِكُوهُنَّ فِي الْبُيُوتِ حَتَّىٰ يَتَوَفَّاهُنَّ الْمَوْتُ أَوْ يَجْعَلَ اللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suka je wa alfăsha daga mătanku, to, ku nẽmi Shaidar mutăne huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidăje har mutuwa ta karɓi răyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su.

Ayah   4:16   الأية
وَاللَّذَانِ يَأْتِيَانِهَا مِنكُمْ فَآذُوهُمَا ۖ فَإِن تَابَا وَأَصْلَحَا فَأَعْرِضُوا عَنْهُمَا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ تَوَّابًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Kuma waɗanda (mază biyu) suka je mata daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan idan sun tũba kuma suka kyautata hălăyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu. Lalle ne Allah Yă kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai

Ayah   4:17   الأية
إِنَّمَا التَّوْبَةُ عَلَى اللَّهِ لِلَّذِينَ يَعْمَلُونَ السُّوءَ بِجَهَالَةٍ ثُمَّ يَتُوبُونَ مِن قَرِيبٍ فَأُولَٰئِكَ يَتُوبُ اللَّهُ عَلَيْهِمْ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Hausa
 
Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatăwar mugun aiki da jăhilci sa'an nan su tũba nan kusa to, waɗannan Allah Yană karɓar tũ barsu kuma Allah Yă kasance Masani ne, Mai hikima.

Ayah   4:18   الأية
وَلَيْسَتِ التَّوْبَةُ لِلَّذِينَ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ حَتَّىٰ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ الْمَوْتُ قَالَ إِنِّي تُبْتُ الْآنَ وَلَا الَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمْ كُفَّارٌ ۚ أُولَٰئِكَ أَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا
Hausa
 
Bă tũba ba ce ga waɗanda suke aikatăwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tũba yanzu," kuma bă tũba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhăli kuwa sună kăfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azăba mai raɗaɗi

Ayah   4:19   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا يَحِلُّ لَكُمْ أَن تَرِثُوا النِّسَاءَ كَرْهًا ۖ وَلَا تَعْضُلُوهُنَّ لِتَذْهَبُوا بِبَعْضِ مَا آتَيْتُمُوهُنَّ إِلَّا أَن يَأْتِينَ بِفَاحِشَةٍ مُّبَيِّنَةٍ ۚ وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ فَإِن كَرِهْتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ اللَّهُ فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا
Hausa
 
Ku waɗanda suka yi ĩmăni! Bă ya halatta a gare ku, ku găji mătă a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dőmin ku tafi da săshen abin da kuka ba su, făce idan suka zo da wata alfăsha bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammănin ku ƙi wani abu alhăli kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa.

Ayah   4:20   الأية
وَإِنْ أَرَدتُّمُ اسْتِبْدَالَ زَوْجٍ مَّكَانَ زَوْجٍ وَآتَيْتُمْ إِحْدَاهُنَّ قِنطَارًا فَلَا تَأْخُذُوا مِنْهُ شَيْئًا ۚ أَتَأْخُذُونَهُ بُهْتَانًا وَإِثْمًا مُّبِينًا
Hausa
 
Kuma idan kun yi nufin musanya măta a matsayin wata măta, alhăli kuwa kun bai wa ɗayarsu ƙinɗari to kada ku karɓi kőme daga gare, shi, shin, ză ku karɓe shi da ƙarya da zunubi băyyananne?

Ayah   4:21   الأية
وَكَيْفَ تَأْخُذُونَهُ وَقَدْ أَفْضَىٰ بَعْضُكُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ وَأَخَذْنَ مِنكُم مِّيثَاقًا غَلِيظًا
Hausa
 
Kuma yăyă ză ku karɓe shi alhăli kuwa, haƙĩƙa, săshenkuyă sădu zuwa ga săshe, kuma sun riƙi alkawari mai kauri daga gare ku?

Ayah   4:22   الأية
وَلَا تَنكِحُوا مَا نَكَحَ آبَاؤُكُم مِّنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۚ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَمَقْتًا وَسَاءَ سَبِيلًا
Hausa
 
Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mătă, făce abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfăsha da abin ƙyăma. Kuma ya mũnana ya zama hanya.

Ayah   4:23   الأية
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُم مِّنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي حُجُورِكُم مِّن نِّسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُم بِهِنَّ فَإِن لَّمْ تَكُونُوا دَخَلْتُم بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَن تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
An haramta muku uwăyenku, da 'yă'yanku, da 'yan'uwanku mătă, da goggonninku, da innoninku, da 'yă'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwăyenku waɗanan da suka shăyar da ku măma, da 'yan'uwanku mătă na shan măma, da uwăyen mătanku, da agőlolinku waɗanda suke cikin ɗăkunanku daga mătanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, băbu laifi a kanku, da mătan 'yă'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mătă, făce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yă kasance Mai găfara ne Mai jin ƙai.

Ayah   4:24   الأية
وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۖ كِتَابَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ ۚ وَأُحِلَّ لَكُم مَّا وَرَاءَ ذَٰلِكُمْ أَن تَبْتَغُوا بِأَمْوَالِكُم مُّحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ ۚ فَمَا اسْتَمْتَعْتُم بِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً ۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا تَرَاضَيْتُم بِهِ مِن بَعْدِ الْفَرِيضَةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا
Hausa
 
Da tsararrun auren wasu maza, făce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littăfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyőyinku, kună măsu yin aure, bă măsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bă su ijărőrinsu bisa farillar sadăki. Băbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya da shi a băyan farillar sadăki. Lalle ne Allah Yă kasance Masani ne, Mai hikima.

Ayah   4:25   الأية
وَمَن لَّمْ يَسْتَطِعْ مِنكُمْ طَوْلًا أَن يَنكِحَ الْمُحْصَنَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ فَمِن مَّا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُم مِّن فَتَيَاتِكُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ۚ وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِإِيمَانِكُم ۚ بَعْضُكُم مِّن بَعْضٍ ۚ فَانكِحُوهُنَّ بِإِذْنِ أَهْلِهِنَّ وَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ مُحْصَنَاتٍ غَيْرَ مُسَافِحَاتٍ وَلَا مُتَّخِذَاتِ أَخْدَانٍ ۚ فَإِذَا أُحْصِنَّ فَإِنْ أَتَيْنَ بِفَاحِشَةٍ فَعَلَيْهِنَّ نِصْفُ مَا عَلَى الْمُحْصَنَاتِ مِنَ الْعَذَابِ ۚ ذَٰلِكَ لِمَنْ خَشِيَ الْعَنَتَ مِنكُمْ ۚ وَأَن تَصْبِرُوا خَيْرٌ لَّكُمْ ۗ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Hausa
 
Kuma wanda bai sămi wadăta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya aura)daga abin da hannuwanku na dăma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmăninku, săshenku daga săshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutănensu. Kuma ku bă su ijărőrinsu bisa ga abin da aka sani, suna măsu kamun kai bă măsu zina ba, kuma bă măsu riƙon abőkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfăsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azăba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsőron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai găfara ne Mai jin ƙai.

Ayah   4:26   الأية
يُرِيدُ اللَّهُ لِيُبَيِّنَ لَكُمْ وَيَهْدِيَكُمْ سُنَنَ الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ وَيَتُوبَ عَلَيْكُمْ ۗ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Hausa
 
Allah Yană nufin Ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyőyin waɗanda suke a gabăninku kuma Ya karɓi tũbarku. Kuma Allah Masani ne Mai hikima.

Ayah   4:27   الأية
وَاللَّهُ يُرِيدُ أَن يَتُوبَ عَلَيْكُمْ وَيُرِيدُ الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ الشَّهَوَاتِ أَن تَمِيلُوا مَيْلًا عَظِيمًا
Hausa
 
Kuma Allah Yană nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha'awőyi suna nufin ku karkata, karkata mai girma.

Ayah   4:28   الأية
يُرِيدُ اللَّهُ أَن يُخَفِّفَ عَنكُمْ ۚ وَخُلِقَ الْإِنسَانُ ضَعِيفًا
Hausa
 
Allah Yana nufin Ya yi muku sauƙi, kuma an halitta mutum yana mai rauni.

Ayah   4:29   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَأْكُلُوا أَمْوَالَكُم بَيْنَكُم بِالْبَاطِلِ إِلَّا أَن تَكُونَ تِجَارَةً عَن تَرَاضٍ مِّنكُمْ ۚ وَلَا تَقْتُلُوا أَنفُسَكُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ بِكُمْ رَحِيمًا
Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku ci dũkiyőyinku a tsakăninku da yaudara, făce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kănku. Lalle ne Allah Yă kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne.

Ayah   4:30   الأية
وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ عُدْوَانًا وَظُلْمًا فَسَوْفَ نُصْلِيهِ نَارًا ۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرًا
Hausa
 
Wanda ya aikata wancan bisa ta'adi da zălunci, to, ză Mu ƙőne shi da Wuta. Kuma wannan yă kasance ga Allah (abu ne) mai sauƙi.

Ayah   4:31   الأية
إِن تَجْتَنِبُوا كَبَائِرَ مَا تُنْهَوْنَ عَنْهُ نُكَفِّرْ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَنُدْخِلْكُم مُّدْخَلًا كَرِيمًا
Hausa
 
Idan kuka nĩsanci manyan abubuwan da ake hana ku aikatăwa, to, ză Mu kankare mũnanan ayyukanku daga gare ku, kuma Mu shigar da ku mashiga ta karimci.

Ayah   4:32   الأية
وَلَا تَتَمَنَّوْا مَا فَضَّلَ اللَّهُ بِهِ بَعْضَكُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ ۚ لِّلرِّجَالِ نَصِيبٌ مِّمَّا اكْتَسَبُوا ۖ وَلِلنِّسَاءِ نَصِيبٌ مِّمَّا اكْتَسَبْنَ ۚ وَاسْأَلُوا اللَّهَ مِن فَضْلِهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمًا
Hausa
 
Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita săshenku da shi a kan săshe; maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mătă suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku rőƙi Allah daga falalarSa. Lalle ne Allah Yă kasance ga dukkan kőme, Masani.

Ayah   4:33   الأية
وَلِكُلٍّ جَعَلْنَا مَوَالِيَ مِمَّا تَرَكَ الْوَالِدَانِ وَالْأَقْرَبُونَ ۚ وَالَّذِينَ عَقَدَتْ أَيْمَانُكُمْ فَآتُوهُمْ نَصِيبَهُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدًا
Hausa
 
Kuma ga kőwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwőyinku suka ƙulla ku bă su rabonsu. Lalle ne, Allah Yă kasance, a kan dukkan kőme, Mahalarci.

Ayah   4:34   الأية
الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ وَبِمَا أَنفَقُوا مِنْ أَمْوَالِهِمْ ۚ فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ حَافِظَاتٌ لِّلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ اللَّهُ ۚ وَاللَّاتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَاهْجُرُوهُنَّ فِي الْمَضَاجِعِ وَاضْرِبُوهُنَّ ۖ فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيًّا كَبِيرًا
Hausa
 
Maza măsu tsayuwa ne a kan mătă, sabőda abin da Allah Ya fifita săshensu da shi a kan săshe kuma sabőda abin da suka ciyar daga dũkiyőyinsu. To, sălihanmătă măsu ɗă'a ne, măsu tsarẽwa ga gaibi sabőda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsőron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurăren kwanciya, kuma ku dőke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yă kasance Maɗaukaki, Mai girma.

Ayah   4:35   الأية
وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوا حَكَمًا مِّنْ أَهْلِهِ وَحَكَمًا مِّنْ أَهْلِهَا إِن يُرِيدَا إِصْلَاحًا يُوَفِّقِ اللَّهُ بَيْنَهُمَا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا
Hausa
 
Kuma idan kun ji tsőron săɓăwar tsakăninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutănensa da wani mai sulhu daga mutănenta. Idan sun yi nufin gyărăwa, Allah zai daidaita tsakăninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yă kasance Masani Mai jarrabăwa.

Ayah   4:36   الأية
وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا ۖ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا وَبِذِي الْقُرْبَىٰ وَالْيَتَامَىٰ وَالْمَسَاكِينِ وَالْجَارِ ذِي الْقُرْبَىٰ وَالْجَارِ الْجُنُبِ وَالصَّاحِبِ بِالْجَنبِ وَابْنِ السَّبِيلِ وَمَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ مُخْتَالًا فَخُورًا
Hausa
 
Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatăwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marăyu da matalauta, da maƙwabci ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abőki a gẽfe da ɗan hanya, da abin da hannuwanku na dăma suka mallaka. Lalle ne Allah bă Ya son wanda ya kasance mai tăƙama, mai yawan alfahari.

Ayah   4:37   الأية
الَّذِينَ يَبْخَلُونَ وَيَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبُخْلِ وَيَكْتُمُونَ مَا آتَاهُمُ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ ۗ وَأَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا مُّهِينًا
Hausa
 
Waɗanda suke yin rőwa, kuma sună umurnin mutăne da yin rőwa, kuma suna ɓőyewar abin da Allah Ya bă su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, sabőda kăfirai, azăba mai walăkantarwa.

Ayah   4:38   الأية
وَالَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ رِئَاءَ النَّاسِ وَلَا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَلَا بِالْيَوْمِ الْآخِرِ ۗ وَمَن يَكُنِ الشَّيْطَانُ لَهُ قَرِينًا فَسَاءَ قَرِينًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyőyinsu dőmin nũna wa mutăne, kuma bă su yin ĩmăni da Allah, kuma bă su yin ĩmănida Rănar Lăhira kuma wanda Shaiɗan ya kasance abőkin haɗi a gare shi, to, yă mũnana ga abőkinhaɗi.

Ayah   4:39   الأية
وَمَاذَا عَلَيْهِمْ لَوْ آمَنُوا بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَأَنفَقُوا مِمَّا رَزَقَهُمُ اللَّهُ ۚ وَكَانَ اللَّهُ بِهِمْ عَلِيمًا
Hausa
 
Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmăni da Allah, kumada Rănar Lăhira, kuma sun ciyar da abin da Allah Yă azurtă su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani?

Ayah   4:40   الأية
إِنَّ اللَّهَ لَا يَظْلِمُ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ ۖ وَإِن تَكُ حَسَنَةً يُضَاعِفْهَا وَيُؤْتِ مِن لَّدُنْهُ أَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
Lalle ne, Allah bă Ya zăluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alhẽri ce, zai riɓanya ta, kuma Ya kăwo daga gunsa ijăra mai girma.

Ayah   4:41   الأية
فَكَيْفَ إِذَا جِئْنَا مِن كُلِّ أُمَّةٍ بِشَهِيدٍ وَجِئْنَا بِكَ عَلَىٰ هَٰؤُلَاءِ شَهِيدًا
Hausa
 
To, yăyă, idan Mun zo da shaidu daga dukkan al'umma, kuma Muka zo da kai a kan waɗannan, kana mai shaida!

Ayah   4:42   الأية
يَوْمَئِذٍ يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَعَصَوُا الرَّسُولَ لَوْ تُسَوَّىٰ بِهِمُ الْأَرْضُ وَلَا يَكْتُمُونَ اللَّهَ حَدِيثًا
Hausa
 
A rănar nan, waɗanda suka kăfirta kuma suka săɓă wa Manzo, sună gũrin dă an baje ƙasa dasu, kuma bă su ɓőye wa Allah wani labări.

Ayah   4:43   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْرَبُوا الصَّلَاةَ وَأَنتُمْ سُكَارَىٰ حَتَّىٰ تَعْلَمُوا مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغْتَسِلُوا ۚ وَإِن كُنتُم مَّرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ مِّنكُم مِّنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا
Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku kusanci salla alhăli kuwa kuna măsu măye, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna măsu janaba, făce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kăshi, kő kuwa kun shăfi mătă ba ku sămi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shăfa ga fuskokinku da hannuwanku . Lalle ne Allah Yă kasance Mai yăfẽwa Mai găfara.

Ayah   4:44   الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ أُوتُوا نَصِيبًا مِّنَ الْكِتَابِ يَشْتَرُونَ الضَّلَالَةَ وَيُرِيدُونَ أَن تَضِلُّوا السَّبِيلَ
Hausa
 
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo daga Littafi, suna sayen ɓata, kuma suna nẽman ku ɓace daga hanya?

Ayah   4:45   الأية
وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِأَعْدَائِكُمْ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ وَلِيًّا وَكَفَىٰ بِاللَّهِ نَصِيرًا
Hausa
 
Kuma Allah ne Mafi sani ga maƙiyanku, kuma Allah Yă isa Ya zama Majibinci, kuma Yă isa Ya zama Mataimaki.

Ayah   4:46   الأية
مِّنَ الَّذِينَ هَادُوا يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِ وَيَقُولُونَ سَمِعْنَا وَعَصَيْنَا وَاسْمَعْ غَيْرَ مُسْمَعٍ وَرَاعِنَا لَيًّا بِأَلْسِنَتِهِمْ وَطَعْنًا فِي الدِّينِ ۚ وَلَوْ أَنَّهُمْ قَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا وَاسْمَعْ وَانظُرْنَا لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ وَأَقْوَمَ وَلَٰكِن لَّعَنَهُمُ اللَّهُ بِكُفْرِهِمْ فَلَا يُؤْمِنُونَ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sună karkatar da magana daga wurărenta suna cẽwa: "Munjiya kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyăwa, kuma ră'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," dőmin karkatarwa da harsunansu, kuma dőmin sũkă a cikin addini. Kuma dă lalle sũ, sun ce: "Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurăra kuma ka dăkata mana," haƙĩƙa, dă ya kasance mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yă la'anẽ su, sabőda kăfircinsu don haka bă ză su yi ĩmăni ba, sai kaɗan.

Ayah   4:47   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ آمِنُوا بِمَا نَزَّلْنَا مُصَدِّقًا لِّمَا مَعَكُم مِّن قَبْلِ أَن نَّطْمِسَ وُجُوهًا فَنَرُدَّهَا عَلَىٰ أَدْبَارِهَا أَوْ نَلْعَنَهُمْ كَمَا لَعَنَّا أَصْحَابَ السَّبْتِ ۚ وَكَانَ أَمْرُ اللَّهِ مَفْعُولًا
Hausa
 
Yă kũ waɗanda aka bai wa Littăfi! Ku yi ĩmăni da abinda Muka saukar, yana mai gaskatăwa ga abin da yake tăre da ku, tun gabanin Mu shăfe wasu fuskőki, sa'an nan Mu mayar da su a kan băyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatăwa.

Ayah   4:48   الأية
إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَاءُ ۚ وَمَن يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدِ افْتَرَىٰ إِثْمًا عَظِيمًا
Hausa
 
Lalle ne, Allah ba Ya găfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana găfarta abin da yake băyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma.

Ayah   4:49   الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يُزَكُّونَ أَنفُسَهُم ۚ بَلِ اللَّهُ يُزَكِّي مَن يَشَاءُ وَلَا يُظْلَمُونَ فَتِيلًا
Hausa
 
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ă'a, Allah ne Yake tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba.

Ayah   4:50   الأية
انظُرْ كَيْفَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ ۖ وَكَفَىٰ بِهِ إِثْمًا مُّبِينًا
Hausa
 
Ka dũba yadda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah! Kuma shi ya isa ga zama zunubi bayyananne.

Ayah   4:51   الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ أُوتُوا نَصِيبًا مِّنَ الْكِتَابِ يُؤْمِنُونَ بِالْجِبْتِ وَالطَّاغُوتِ وَيَقُولُونَ لِلَّذِينَ كَفَرُوا هَٰؤُلَاءِ أَهْدَىٰ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا سَبِيلًا
Hausa
 
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabő da ga Littafi suna ĩmăni da gunki da Shaiɗan kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kăfirta: "Waɗannan ne mafiya shiriya daga waɗanda suka yi ĩmăni ga hanya"?

Ayah   4:52   الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَعَنَهُمُ اللَّهُ ۖ وَمَن يَلْعَنِ اللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُ نَصِيرًا
Hausa
 
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bă ză ka sămi mataimaki a gare shi ba.

Ayah   4:53   الأية
أَمْ لَهُمْ نَصِيبٌ مِّنَ الْمُلْكِ فَإِذًا لَّا يُؤْتُونَ النَّاسَ نَقِيرًا
Hausa
 
Ko suna da rabő ne daga mulki? To, a sa'an nan bă ză su iya bai wa mutăne hancin gurtsun dabino ba.

Ayah   4:54   الأية
أَمْ يَحْسُدُونَ النَّاسَ عَلَىٰ مَا آتَاهُمُ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ ۖ فَقَدْ آتَيْنَا آلَ إِبْرَاهِيمَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَآتَيْنَاهُم مُّلْكًا عَظِيمًا
Hausa
 
Ko suna hăsadar mutăne ne a kan abin da Allah Ya bă su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrăhĩm Littăfida hikima kuma Mun bă su mulki mai girma.

Ayah   4:55   الأية
فَمِنْهُم مَّنْ آمَنَ بِهِ وَمِنْهُم مَّن صَدَّ عَنْهُ ۚ وَكَفَىٰ بِجَهَنَّمَ سَعِيرًا
Hausa
 
To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmăni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yă isa Jahannama ta hũru da shi.

Ayah   4:56   الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا سَوْفَ نُصْلِيهِمْ نَارًا كُلَّمَا نَضِجَتْ جُلُودُهُم بَدَّلْنَاهُمْ جُلُودًا غَيْرَهَا لِيَذُوقُوا الْعَذَابَ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَزِيزًا حَكِيمًا
Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka kăfirta da ayőyinMu za Mu ƙőne su da wuta, kő da yaushe fătunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fătun, dőmin su ɗanɗani azăba. Lalle ne Allah Yă kasance Mabuwăyi, Mai hikima.

Ayah   4:57   الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَنُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ لَّهُمْ فِيهَا أَزْوَاجٌ مُّطَهَّرَةٌ ۖ وَنُدْخِلُهُمْ ظِلًّا ظَلِيلًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suka yiĩmăni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, ză Mu shigar da su gidăjen Aljanna, (waɗanda) ƙőramu sună gudăna daga ƙarƙashinsu, sună dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mătan aure măsu tsarki, Kuma Mună shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.

Ayah   4:58   الأية
إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَن تُؤَدُّوا الْأَمَانَاتِ إِلَىٰ أَهْلِهَا وَإِذَا حَكَمْتُم بَيْنَ النَّاسِ أَن تَحْكُمُوا بِالْعَدْلِ ۚ إِنَّ اللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ سَمِيعًا بَصِيرًا
Hausa
 
Lalle ne Allah Yană umurnin ku ku băyar da amănőni zuwa ga măsu sũ. Kuma idan kun yi hukunci a tsakănin mutăne, ku yi hukunci da ădalci. Lalle ne Allah mădalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yă kasance Mai ji ne, Mai gani.

Ayah   4:59   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنكُمْ ۖ فَإِن تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا
Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yiĩmăni! Ku yi ɗă'a ga Allah, kuma ku yi ɗă'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jăyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kună ĩmăni da Allah da Rănar Lăhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.

Ayah   4:60   الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَن يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَن يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا بَعِيدًا
Hausa
 
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyăwar cẽwa sună ĩmăni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabăninka, sună nufin su kai ƙăra zuwa ga ¦ăgũtu alhăli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kăfirta da shi, kuma Shaiɗan yană nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.

Ayah   4:61   الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا إِلَىٰ مَا أَنزَلَ اللَّهُ وَإِلَى الرَّسُولِ رَأَيْتَ الْمُنَافِقِينَ يَصُدُّونَ عَنكَ صُدُودًا
Hausa
 
Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo" ză ka ga munăfukai sună kange mutăne daga gare ka, kangẽwa.

Ayah   4:62   الأية
فَكَيْفَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ ثُمَّ جَاءُوكَ يَحْلِفُونَ بِاللَّهِ إِنْ أَرَدْنَا إِلَّا إِحْسَانًا وَتَوْفِيقًا
Hausa
 
To, yaya, idan wata masĩfa ta săme su, sabőda abin da hannuwansu suka gabătar sa'an nan kuma su je maka sună rantsuwa da Allah cẽwa, "Ba mu yi nufin kőme ba sai kyautatawa da daidaităwa."?

Ayah   4:63   الأية
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ يَعْلَمُ اللَّهُ مَا فِي قُلُوبِهِمْ فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ وَعِظْهُمْ وَقُل لَّهُمْ فِي أَنفُسِهِمْ قَوْلًا بَلِيغًا
Hausa
 
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukătansu. Sabőda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasăha.

Ayah   4:64   الأية
وَمَا أَرْسَلْنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذْنِ اللَّهِ ۚ وَلَوْ أَنَّهُمْ إِذ ظَّلَمُوا أَنفُسَهُمْ جَاءُوكَ فَاسْتَغْفَرُوا اللَّهَ وَاسْتَغْفَرَ لَهُمُ الرَّسُولُ لَوَجَدُوا اللَّهَ تَوَّابًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba făce dőmin a yi masa ɗă'a da izinin Allah. Kuma dă dai lalle sũ a lőkacin da suka zălunci kansu, sun zo maka sa'an nan suka nẽmi găfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu găfara, haƙĩƙa, dă sun sămi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.

Ayah   4:65   الأية
فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ لَا يَجِدُوا فِي أَنفُسِهِمْ حَرَجًا مِّمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا تَسْلِيمًا
Hausa
 
To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmăni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya săɓa a tsakăninsu, sa'an nan kuma ba su sămi wani ƙunci a cikin zukătansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamăwa.

Ayah   4:66   الأية
وَلَوْ أَنَّا كَتَبْنَا عَلَيْهِمْ أَنِ اقْتُلُوا أَنفُسَكُمْ أَوِ اخْرُجُوا مِن دِيَارِكُم مَّا فَعَلُوهُ إِلَّا قَلِيلٌ مِّنْهُمْ ۖ وَلَوْ أَنَّهُمْ فَعَلُوا مَا يُوعَظُونَ بِهِ لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ وَأَشَدَّ تَثْبِيتًا
Hausa
 
Kuma dă dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, "Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita daga gidăjenku," dă ba su aikata shi ba, făce kaɗan daga gare su. Kuma dă dai lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dă yă kasance mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa.

Ayah   4:67   الأية
وَإِذًا لَّآتَيْنَاهُم مِّن لَّدُنَّا أَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
Kuma a sa'an nan, haƙĩƙa, dă Mun bă su, lăda mai girma, daga gunMu.

Ayah   4:68   الأية
وَلَهَدَيْنَاهُمْ صِرَاطًا مُّسْتَقِيمًا
Hausa
 
Kuma lalle ne, dă Mun shiryar da su hanya madaidaiciya.

Ayah   4:69   الأية
وَمَن يُطِعِ اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَأُولَٰئِكَ مَعَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِم مِّنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ ۚ وَحَسُنَ أُولَٰئِكَ رَفِيقًا
Hausa
 
Kuma waɗannan da suka yi ɗă'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sună tăre da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabăwa da măsu yawan gaskatăwa, da masu shahăda da sălihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abőkan tafiya.

Ayah   4:70   الأية
ذَٰلِكَ الْفَضْلُ مِنَ اللَّهِ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ عَلِيمًا
Hausa
 
Waccan falalar daga Allah take, kuma Allah Yă isa zama Masani.

Ayah   4:71   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا خُذُوا حِذْرَكُمْ فَانفِرُوا ثُبَاتٍ أَوِ انفِرُوا جَمِيعًا
Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Ku riƙi shirinku sa'an nan ku fitar da hari jama'a, jama'a ko ku fitar da yaƙi gaba ɗaya.

Ayah   4:72   الأية
وَإِنَّ مِنكُمْ لَمَن لَّيُبَطِّئَنَّ فَإِنْ أَصَابَتْكُم مُّصِيبَةٌ قَالَ قَدْ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيَّ إِذْ لَمْ أَكُن مَّعَهُمْ شَهِيدًا
Hausa
 
Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai făsarwa . To idan wata masĩfa ta săme ku, sai ya ce: "Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dőmin ban kasance mahalarci tăre da su ba."

Ayah   4:73   الأية
وَلَئِنْ أَصَابَكُمْ فَضْلٌ مِّنَ اللَّهِ لَيَقُولَنَّ كَأَن لَّمْ تَكُن بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُ مَوَدَّةٌ يَا لَيْتَنِي كُنتُ مَعَهُمْ فَأَفُوزَ فَوْزًا عَظِيمًا
Hausa
 
Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta săme ku haƙĩƙa, tabbas, yană cẽwa, kamar wata sőyayya ba ta kasance a tsakăninku da shi ba: "Yă kaitona! Dă na zama tăre da su dai, dőmin in rabonta da rabő mai girma!"

Ayah   4:74   الأية
فَلْيُقَاتِلْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ الَّذِينَ يَشْرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا بِالْآخِرَةِ ۚ وَمَن يُقَاتِلْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَيُقْتَلْ أَوْ يَغْلِبْ فَسَوْفَ نُؤْتِيهِ أَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lăhira su yi yăƙi, a cikin hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yăki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa ya rinjăya, sa'an nan ză Mu ba shi ijăra mai girma.

Ayah   4:75   الأية
وَمَا لَكُمْ لَا تُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَالْمُسْتَضْعَفِينَ مِنَ الرِّجَالِ وَالنِّسَاءِ وَالْوِلْدَانِ الَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا أَخْرِجْنَا مِنْ هَٰذِهِ الْقَرْيَةِ الظَّالِمِ أَهْلُهَا وَاجْعَل لَّنَا مِن لَّدُنكَ وَلِيًّا وَاجْعَل لَّنَا مِن لَّدُنكَ نَصِيرًا
Hausa
 
Kuma mẽne ne ya săme ku, bă ku yin yăƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yăra sună cewa: "Yă Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutănenta suke da zălunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa."?

Ayah   4:76   الأية
الَّذِينَ آمَنُوا يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ ۖ وَالَّذِينَ كَفَرُوا يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ الطَّاغُوتِ فَقَاتِلُوا أَوْلِيَاءَ الشَّيْطَانِ ۖ إِنَّ كَيْدَ الشَّيْطَانِ كَانَ ضَعِيفًا
Hausa
 
Waɗanda suka yi ĩmăni, sună yăki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kăfirta sună yăƙi a cikin hanyar ¦ăgũtu (Shaiɗan). To, ku yăƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan yă kasance mai rauni.

Ayah   4:77   الأية
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ قِيلَ لَهُمْ كُفُّوا أَيْدِيَكُمْ وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيْهِمُ الْقِتَالُ إِذَا فَرِيقٌ مِّنْهُمْ يَخْشَوْنَ النَّاسَ كَخَشْيَةِ اللَّهِ أَوْ أَشَدَّ خَشْيَةً ۚ وَقَالُوا رَبَّنَا لِمَ كَتَبْتَ عَلَيْنَا الْقِتَالَ لَوْلَا أَخَّرْتَنَا إِلَىٰ أَجَلٍ قَرِيبٍ ۗ قُلْ مَتَاعُ الدُّنْيَا قَلِيلٌ وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ لِّمَنِ اتَّقَىٰ وَلَا تُظْلَمُونَ فَتِيلًا
Hausa
 
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku băyar da zakka."? To a lőkacin da aka wajabta musu yăƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sună tsőron mutăne kamar tsőron Allah kő kuwa mafi tsanani ga tsőron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yăƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dăɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lăhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bă a zăluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!

Ayah   4:78   الأية
أَيْنَمَا تَكُونُوا يُدْرِككُّمُ الْمَوْتُ وَلَوْ كُنتُمْ فِي بُرُوجٍ مُّشَيَّدَةٍ ۗ وَإِن تُصِبْهُمْ حَسَنَةٌ يَقُولُوا هَٰذِهِ مِنْ عِندِ اللَّهِ ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ يَقُولُوا هَٰذِهِ مِنْ عِندِكَ ۚ قُلْ كُلٌّ مِّنْ عِندِ اللَّهِ ۖ فَمَالِ هَٰؤُلَاءِ الْقَوْمِ لَا يَكَادُونَ يَفْقَهُونَ حَدِيثًا
Hausa
 
"Inda duk kuka kasance, mutuwa ză ta riske ku, kuma kő da kun kasance ne a cikin gănuwőyi ingătattu!"Kuma idan wani alhẽri ya săme su sai su ce: "Wannan daga wurin Allah ne," kuma idan wata cũta ta săme su, sai su ce: "Wannan daga gare ka ne."Ka ce: "Dukkansu daga Allah ne." To, me ya sămi waɗannan mutăne, bă su kusantar fahimtar magana?

Ayah   4:79   الأية
مَّا أَصَابَكَ مِنْ حَسَنَةٍ فَمِنَ اللَّهِ ۖ وَمَا أَصَابَكَ مِن سَيِّئَةٍ فَمِن نَّفْسِكَ ۚ وَأَرْسَلْنَاكَ لِلنَّاسِ رَسُولًا ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ شَهِيدًا
Hausa
 
Abin da ya săme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya săme ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutăne, (kana) Manzo, kuma Allah Yă isa ga zama shaida.

Ayah   4:80   الأية
مَّن يُطِعِ الرَّسُولَ فَقَدْ أَطَاعَ اللَّهَ ۖ وَمَن تَوَلَّىٰ فَمَا أَرْسَلْنَاكَ عَلَيْهِمْ حَفِيظًا
Hausa
 
Wanda ya yi ɗă'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yă yi ɗă'a ga Allah. Kuma wanda ya jũya băya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu.

Ayah   4:81   الأية
وَيَقُولُونَ طَاعَةٌ فَإِذَا بَرَزُوا مِنْ عِندِكَ بَيَّتَ طَائِفَةٌ مِّنْهُمْ غَيْرَ الَّذِي تَقُولُ ۖ وَاللَّهُ يَكْتُبُ مَا يُبَيِّتُونَ ۖ فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ وَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ وَكِيلًا
Hausa
 
Kuma sună cẽwa, "Dă'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwăna da niyyar wanin abin da take faɗa, alhăli kuwa Allah na rubũta abin da suke kwăna da niyyarsa. Sabőda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dőgara ga Allah, kuma Allah Yă isa ya zama wakĩli.

Ayah   4:82   الأية
أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ الْقُرْآنَ ۚ وَلَوْ كَانَ مِنْ عِندِ غَيْرِ اللَّهِ لَوَجَدُوا فِيهِ اخْتِلَافًا كَثِيرًا
Hausa
 
Shin, bă su kula da Alƙur'ăni, kuma dă yă kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dă sun sămu, a cikinsa, săɓă wa jũnamai yawa?

Ayah   4:83   الأية
وَإِذَا جَاءَهُمْ أَمْرٌ مِّنَ الْأَمْنِ أَوِ الْخَوْفِ أَذَاعُوا بِهِ ۖ وَلَوْ رَدُّوهُ إِلَى الرَّسُولِ وَإِلَىٰ أُولِي الْأَمْرِ مِنْهُمْ لَعَلِمَهُ الَّذِينَ يَسْتَنبِطُونَهُ مِنْهُمْ ۗ وَلَوْلَا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ لَاتَّبَعْتُمُ الشَّيْطَانَ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Kuma idan wani al'amari daga aminci ko tsőro ya je musu, sai su wătsa shi. Dă sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, ză su san shi. Kuma bă dőmin falalar Allah bă a kanku da rahamarSa, haƙĩƙa, dă kun bi Shaiɗan făce kaɗan.

Ayah   4:84   الأية
فَقَاتِلْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ لَا تُكَلَّفُ إِلَّا نَفْسَكَ ۚ وَحَرِّضِ الْمُؤْمِنِينَ ۖ عَسَى اللَّهُ أَن يَكُفَّ بَأْسَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ وَاللَّهُ أَشَدُّ بَأْسًا وَأَشَدُّ تَنكِيلًا
Hausa
 
Sabőda haka, ka yi yăƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a kanka, kuma ka kwaɗaitar da mũminai. Akwai tsammănin Allah Ya kange găfin waɗanda suka kăfirta, kuma Allah ne Mafi tsananin găfi, kuma Mafi tsananin azabtăwa.

Ayah   4:85   الأية
مَّن يَشْفَعْ شَفَاعَةً حَسَنَةً يَكُن لَّهُ نَصِيبٌ مِّنْهَا ۖ وَمَن يَشْفَعْ شَفَاعَةً سَيِّئَةً يَكُن لَّهُ كِفْلٌ مِّنْهَا ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ مُّقِيتًا
Hausa
 
Wanda ya yi cẽto, cẽto mai kyau, zai sămi rabo daga gare shi, kuma wanda ya yi cẽto,cẽto mummũna, zai sămi ma'aunidaga gare shi, Kuma Allah Yă kasance, a kan dukkan kőme, Mai ƙayyade lőkaci.

Ayah   4:86   الأية
وَإِذَا حُيِّيتُم بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوا بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ حَسِيبًا
Hausa
 
Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, kő kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yă kasance a kan dukkan kőme Mai lissăfi.

Ayah   4:87   الأية
اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ لَيَجْمَعَنَّكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ لَا رَيْبَ فِيهِ ۗ وَمَنْ أَصْدَقُ مِنَ اللَّهِ حَدِيثًا
Hausa
 
Allah băbu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙĩƙa Yana tăra ku har zuwa ga Yinin ˇiyăma băbu shakka a cikinsa. Kuma wăne ne mafi gaskiya daga Allah ga 1ăbări.

Ayah   4:88   الأية
فَمَا لَكُمْ فِي الْمُنَافِقِينَ فِئَتَيْنِ وَاللَّهُ أَرْكَسَهُم بِمَا كَسَبُوا ۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَهْدُوا مَنْ أَضَلَّ اللَّهُ ۖ وَمَن يُضْلِلِ اللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُ سَبِيلًا
Hausa
 
To, mẽne ne ya săme ku a cikin munăfukai kun zama ƙungiya biyu, alhăli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabőda abin da suka tsirfanta? Shin, kună nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bă ză ka sămi wata hanya ba zuwa gare shi.

Ayah   4:89   الأية
وَدُّوا لَوْ تَكْفُرُونَ كَمَا كَفَرُوا فَتَكُونُونَ سَوَاءً ۖ فَلَا تَتَّخِذُوا مِنْهُمْ أَوْلِيَاءَ حَتَّىٰ يُهَاجِرُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ ۚ فَإِن تَوَلَّوْا فَخُذُوهُمْ وَاقْتُلُوهُمْ حَيْثُ وَجَدتُّمُوهُمْ ۖ وَلَا تَتَّخِذُوا مِنْهُمْ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا
Hausa
 
Suna gũrin ku kăfirta kamar yadda suka kăfirta, dőmin ku kasance daidai. Sabőda haka kada ku riƙi wasu masőya daga cikinsu, sai sun yő hijira a cikin hanyar Allah. Sa'an nan idan sun jũya, to, ku kămă su kuma ku kashe su inda duk kuka săme su. Kuma kada ku riƙi wani masőyi daga gare su ko wani mataimaki.

Ayah   4:90   الأية
إِلَّا الَّذِينَ يَصِلُونَ إِلَىٰ قَوْمٍ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُم مِّيثَاقٌ أَوْ جَاءُوكُمْ حَصِرَتْ صُدُورُهُمْ أَن يُقَاتِلُوكُمْ أَوْ يُقَاتِلُوا قَوْمَهُمْ ۚ وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَسَلَّطَهُمْ عَلَيْكُمْ فَلَقَاتَلُوكُمْ ۚ فَإِنِ اعْتَزَلُوكُمْ فَلَمْ يُقَاتِلُوكُمْ وَأَلْقَوْا إِلَيْكُمُ السَّلَمَ فَمَا جَعَلَ اللَّهُ لَكُمْ عَلَيْهِمْ سَبِيلًا
Hausa
 
Făce dai waɗanda suke săduwa zuwa ga wasu mutăne waɗanda a tsakăninku da su akwai alkawari, kő kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirăzansu sun yi ƙunci ga su yăke ku, kő su yăƙi mutănensu. Kuma dă Allah Yă so lalle ne, dă Yă bă su ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yăke ku. To, idan sun nĩsance ku sa'an nan ba su yăƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu.

Ayah   4:91   الأية
سَتَجِدُونَ آخَرِينَ يُرِيدُونَ أَن يَأْمَنُوكُمْ وَيَأْمَنُوا قَوْمَهُمْ كُلَّ مَا رُدُّوا إِلَى الْفِتْنَةِ أُرْكِسُوا فِيهَا ۚ فَإِن لَّمْ يَعْتَزِلُوكُمْ وَيُلْقُوا إِلَيْكُمُ السَّلَمَ وَيَكُفُّوا أَيْدِيَهُمْ فَخُذُوهُمْ وَاقْتُلُوهُمْ حَيْثُ ثَقِفْتُمُوهُمْ ۚ وَأُولَٰئِكُمْ جَعَلْنَا لَكُمْ عَلَيْهِمْ سُلْطَانًا مُّبِينًا
Hausa
 
Za ku sămi wasu sună nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutănensu, kő da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyă su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kămă su, kuma ku kashe su inda duk kuka kămă su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu.

Ayah   4:92   الأية
وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ أَن يَقْتُلَ مُؤْمِنًا إِلَّا خَطَأً ۚ وَمَن قَتَلَ مُؤْمِنًا خَطَأً فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُّؤْمِنَةٍ وَدِيَةٌ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰ أَهْلِهِ إِلَّا أَن يَصَّدَّقُوا ۚ فَإِن كَانَ مِن قَوْمٍ عَدُوٍّ لَّكُمْ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُّؤْمِنَةٍ ۖ وَإِن كَانَ مِن قَوْمٍ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُم مِّيثَاقٌ فَدِيَةٌ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰ أَهْلِهِ وَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُّؤْمِنَةٍ ۖ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ تَوْبَةً مِّنَ اللَّهِ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Hausa
 
Kuma bă ya kasancẽwa ga mũmini ya kashe wani mũmini, făce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutănensa, ăce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutăne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutăne ne (waɗanda) a tsakăninku da tsakăninsu akwai alkawari, sai ya băyar da diyya ga mutănensa, tare da 'yanta wuya mũmina. To, wanda bai sămi (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jẽre, dőmin tũba daga Allah. Kuma Allah Yă kasance Masani, Mai hikima.

Ayah   4:93   الأية
وَمَن يَقْتُلْ مُؤْمِنًا مُّتَعَمِّدًا فَجَزَاؤُهُ جَهَنَّمُ خَالِدًا فِيهَا وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِ وَلَعَنَهُ وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِيمًا
Hausa
 
Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Yă yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azăba mai girma.

Ayah   4:94   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا ضَرَبْتُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَتَبَيَّنُوا وَلَا تَقُولُوا لِمَنْ أَلْقَىٰ إِلَيْكُمُ السَّلَامَ لَسْتَ مُؤْمِنًا تَبْتَغُونَ عَرَضَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا فَعِندَ اللَّهِ مَغَانِمُ كَثِيرَةٌ ۚ كَذَٰلِكَ كُنتُم مِّن قَبْلُ فَمَنَّ اللَّهُ عَلَيْكُمْ فَتَبَيَّنُوا ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرًا
Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), dőmin jihădi, to, ku nẽmi băyani. Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: "Bă Musulmi kake ba." Kună nẽman hăjar răyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai ganimőmi măsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabănin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Sabőda haka ku zan nẽman bayăni.Lalle ne Allah Yă kasance, ga abin da kuke aikatăwa, Masani.

Ayah   4:95   الأية
لَّا يَسْتَوِي الْقَاعِدُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ غَيْرُ أُولِي الضَّرَرِ وَالْمُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ ۚ فَضَّلَ اللَّهُ الْمُجَاهِدِينَ بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ عَلَى الْقَاعِدِينَ دَرَجَةً ۚ وَكُلًّا وَعَدَ اللَّهُ الْحُسْنَىٰ ۚ وَفَضَّلَ اللَّهُ الْمُجَاهِدِينَ عَلَى الْقَاعِدِينَ أَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
Măsu zama daga barin yăƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da măsu jihădi a cikin hanyar Allah da dũkiyőyinsu da răyukansu, bă su zama daidai. Allah Yă fĩfĩta măsu jihădi da dũkiyoyinsu da răyukansu a kan măsu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Yă yi musu alkawari da abu mai kyau . Kuma Allah yă fĩfĩta măsu jihădi a kan măsu zama da lăda mai girma.

Ayah   4:96   الأية
دَرَجَاتٍ مِّنْهُ وَمَغْفِرَةً وَرَحْمَةً ۚ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Darajőji daga gare Shi da găfara da rahama. Kuma Allah Yă kasance Mai găfara ne, Mai jin ƙai.

Ayah   4:97   الأية
إِنَّ الَّذِينَ تَوَفَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ ظَالِمِي أَنفُسِهِمْ قَالُوا فِيمَ كُنتُمْ ۖ قَالُوا كُنَّا مُسْتَضْعَفِينَ فِي الْأَرْضِ ۚ قَالُوا أَلَمْ تَكُنْ أَرْضُ اللَّهِ وَاسِعَةً فَتُهَاجِرُوا فِيهَا ۚ فَأُولَٰئِكَ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ ۖ وَسَاءَتْ مَصِيرًا
Hausa
 
Lalle ne, waɗanda mală'ĩku suka karɓi răyukansu, (alhăli) sună măsu zăluntar kansu,sun ce (musu): "A cikin me kuka kasance?" (Su kuma) suka ce: "Mun kasance waɗanda aka raunana a cikin ƙasa." Suka ce: "Ashe ƙasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba, dőmin ku yi hijira a cikinta?" To, waɗannan makőmarsu Jahannama ce. Kuma tă mũnana ta zama makőma.

Ayah   4:98   الأية
إِلَّا الْمُسْتَضْعَفِينَ مِنَ الرِّجَالِ وَالنِّسَاءِ وَالْوِلْدَانِ لَا يَسْتَطِيعُونَ حِيلَةً وَلَا يَهْتَدُونَ سَبِيلًا
Hausa
 
Făce waɗanda aka raunana daga maza da mătă da yăra waɗanda bă su iya yin wata dabăra, kuma bă su shiryuwa ga hanya.

Ayah   4:99   الأية
فَأُولَٰئِكَ عَسَى اللَّهُ أَن يَعْفُوَ عَنْهُمْ ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَفُوًّا غَفُورًا
Hausa
 
To, waɗannan akwai tsammănin Allah Ya yăfe laifi daga gare su, kuma Allah Yă kasance Mai yăfẽwa ne, Mai găfara.

Ayah   4:100   الأية
وَمَن يُهَاجِرْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ يَجِدْ فِي الْأَرْضِ مُرَاغَمًا كَثِيرًا وَسَعَةً ۚ وَمَن يَخْرُجْ مِن بَيْتِهِ مُهَاجِرًا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ ثُمَّ يُدْرِكْهُ الْمَوْتُ فَقَدْ وَقَعَ أَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar Allah, zai sămu, a cikin ƙasa, wurăren jũyăwa măsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lădarsa tă auku ga Allah, Kuma Allah Yă kasance, a gare ku, Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah   4:101   الأية
وَإِذَا ضَرَبْتُمْ فِي الْأَرْضِ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَقْصُرُوا مِنَ الصَّلَاةِ إِنْ خِفْتُمْ أَن يَفْتِنَكُمُ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ إِنَّ الْكَافِرِينَ كَانُوا لَكُمْ عَدُوًّا مُّبِينًا
Hausa
 
Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, băbu laifi a kanku ku rage daga salla idan kun ji tsőron waɗanda suka kăfirta su fitine ku. Lalle ne kăfirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne.

Ayah   4:102   الأية
وَإِذَا كُنتَ فِيهِمْ فَأَقَمْتَ لَهُمُ الصَّلَاةَ فَلْتَقُمْ طَائِفَةٌ مِّنْهُم مَّعَكَ وَلْيَأْخُذُوا أَسْلِحَتَهُمْ فَإِذَا سَجَدُوا فَلْيَكُونُوا مِن وَرَائِكُمْ وَلْتَأْتِ طَائِفَةٌ أُخْرَىٰ لَمْ يُصَلُّوا فَلْيُصَلُّوا مَعَكَ وَلْيَأْخُذُوا حِذْرَهُمْ وَأَسْلِحَتَهُمْ ۗ وَدَّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْ تَغْفُلُونَ عَنْ أَسْلِحَتِكُمْ وَأَمْتِعَتِكُمْ فَيَمِيلُونَ عَلَيْكُم مَّيْلَةً وَاحِدَةً ۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِن كَانَ بِكُمْ أَذًى مِّن مَّطَرٍ أَوْ كُنتُم مَّرْضَىٰ أَن تَضَعُوا أَسْلِحَتَكُمْ ۖ وَخُذُوا حِذْرَكُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ أَعَدَّ لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا مُّهِينًا
Hausa
 
Kuma idan kă kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tăre da kai, kuma sai su riƙe makămansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga băyanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tăre da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makămansu. Waɗanda suka kăfirta sun yi gũrin dă dai kuna shagala daga makamanku da kăyanku dőmin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma băbu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, kő kuwa kun kasance măsu jinya ga ku ajiye makămanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Yă yi tattali, ga kăfirai, azăba mai walakantarwa.

Ayah   4:103   الأية
فَإِذَا قَضَيْتُمُ الصَّلَاةَ فَاذْكُرُوا اللَّهَ قِيَامًا وَقُعُودًا وَعَلَىٰ جُنُوبِكُمْ ۚ فَإِذَا اطْمَأْنَنتُمْ فَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ ۚ إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَّوْقُوتًا
Hausa
 
Sa'an nan idan kun ƙăre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan săsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tă kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lőkuta.

Ayah   4:104   الأية
وَلَا تَهِنُوا فِي ابْتِغَاءِ الْقَوْمِ ۖ إِن تَكُونُوا تَأْلَمُونَ فَإِنَّهُمْ يَأْلَمُونَ كَمَا تَأْلَمُونَ ۖ وَتَرْجُونَ مِنَ اللَّهِ مَا لَا يَرْجُونَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Hausa
 
Kuma kada ku sassauta a cikin nẽman mutănen idankun kasance kuna jin zőgi, to, lalle sũ ma, suna jin zőgi kamar yadda kuke jin zőgi. Kuma kuna tsammăni, daga Allah, abin da bă su tsammăni. Kuma Allah Yă kasance Masani Mai hikima.

Ayah   4:105   الأية
إِنَّا أَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِتَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ بِمَا أَرَاكَ اللَّهُ ۚ وَلَا تَكُن لِّلْخَائِنِينَ خَصِيمًا
Hausa
 
Lalle ne, Mũ, Mun saukar , zuwa gare ka, Littăfi da gaskiya, dőmin ka yi hukunci a tsakănin mutăne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma dőmin măsu yaudara.

Ayah   4:106   الأية
وَاسْتَغْفِرِ اللَّهَ ۖ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Kuma ka nẽmi Allah găfara. Lalle ne Allah Yă kasance Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah   4:107   الأية
وَلَا تُجَادِلْ عَنِ الَّذِينَ يَخْتَانُونَ أَنفُسَهُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ خَوَّانًا أَثِيمًا
Hausa
 
Kuma kada ka yi jăyayya dőmin tunkuɗe wa waɗanda suka yaudari kansu. Lalle ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai yawan hă'inci mai yawan zunubi.

Ayah   4:108   الأية
يَسْتَخْفُونَ مِنَ النَّاسِ وَلَا يَسْتَخْفُونَ مِنَ اللَّهِ وَهُوَ مَعَهُمْ إِذْ يُبَيِّتُونَ مَا لَا يَرْضَىٰ مِنَ الْقَوْلِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيطًا
Hausa
 
Suna nẽman ɓőyewa daga mutăne kuma bă su nẽmanɓőyewa daga Allah, alhăli kuwa Shi Yana tăre da su a lőkacin da suke kwăna da niyyar yin abin da bă Ya yarda da shi daga maganar. Kuma Allah Yă kasance ga abin da suke aikatăwa Mai kẽwayẽwa.

Ayah   4:109   الأية
هَا أَنتُمْ هَٰؤُلَاءِ جَادَلْتُمْ عَنْهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا فَمَن يُجَادِلُ اللَّهَ عَنْهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَم مَّن يَكُونُ عَلَيْهِمْ وَكِيلًا
Hausa
 
Gă ku, yă waɗannan ! Kun yi jidăli, dőmin tunkuɗe musu (kunya)a cikin răyuwar dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rănar ˇiyăma? Ko kuwa wăne ne zai kasance wakĩli a kansu?

Ayah   4:110   الأية
وَمَن يَعْمَلْ سُوءًا أَوْ يَظْلِمْ نَفْسَهُ ثُمَّ يَسْتَغْفِرِ اللَّهَ يَجِدِ اللَّهَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Kuma wanda ya aikata cũta kő kuwa ya zălunci kansa, sa'an nan kuma ya nẽmi Allah găfara, zai sămi Allah Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah   4:111   الأية
وَمَن يَكْسِبْ إِثْمًا فَإِنَّمَا يَكْسِبُهُ عَلَىٰ نَفْسِهِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Hausa
 
Kuma wanda ya yi tsirfanci zunubi, to yană tsirfarsa ne a kan kansa kawai. Kuma Allah Yă kasance Masani, Mai hikima.

Ayah   4:112   الأية
وَمَن يَكْسِبْ خَطِيئَةً أَوْ إِثْمًا ثُمَّ يَرْمِ بِهِ بَرِيئًا فَقَدِ احْتَمَلَ بُهْتَانًا وَإِثْمًا مُّبِينًا
Hausa
 
Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi sa'an nan kuma ya jẽfi wani barrantacce da shi, to, lalle ne yă tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne.

Ayah   4:113   الأية
وَلَوْلَا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكَ وَرَحْمَتُهُ لَهَمَّت طَّائِفَةٌ مِّنْهُمْ أَن يُضِلُّوكَ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّا أَنفُسَهُمْ ۖ وَمَا يَضُرُّونَكَ مِن شَيْءٍ ۚ وَأَنزَلَ اللَّهُ عَلَيْكَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَعَلَّمَكَ مَا لَمْ تَكُن تَعْلَمُ ۚ وَكَانَ فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكَ عَظِيمًا
Hausa
 
Kuma bă dőmin falalar Allah ba, a kanka, da rahamarSa, haƙĩƙa, dă wata ƙungiya daga gare su ta himmatu ga su ɓatar da kai. Kuma bă su ɓatarwa făce kansu, kuma bă su cũtar ka daga kőme, Kuma Allah Yă saukar da Littăfi da hikima gare ka, kuma Ya sanar da kai abin da ba ka kasance kă sani ba. Kuma falalar Allah tă kasance mai girma a gare ka.

Ayah   4:114   الأية
لَّا خَيْرَ فِي كَثِيرٍ مِّن نَّجْوَاهُمْ إِلَّا مَنْ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوْ مَعْرُوفٍ أَوْ إِصْلَاحٍ بَيْنَ النَّاسِ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ ابْتِغَاءَ مَرْضَاتِ اللَّهِ فَسَوْفَ نُؤْتِيهِ أَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
Băbu wani alhẽri a cikin măsu yawa daga gănawarsu făce wanda ya yi umurni da wata sadaka kő kuwa wani alhẽri kő kuwa gyăra a tsakănin mutăne. Wanda ya aikata haka dőmin nẽman yardődin Allah to ză Mu bă shi lăda mai girma.

Ayah   4:115   الأية
وَمَن يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَىٰ وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّىٰ وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ ۖ وَسَاءَتْ مَصِيرًا
Hausa
 
Kuma wanda ya săɓă wa Manzo daga băyan shiriya tă bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar mũminai, ză Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙőne shi da Jahannama. Kuma tă mũnana ta zama makőma.

Ayah   4:116   الأية
إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَاءُ ۚ وَمَن يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا
Hausa
 
Lalle ne, Allah ba Ya găfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana găfarta abin da yake băyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nĩsa.

Ayah   4:117   الأية
إِن يَدْعُونَ مِن دُونِهِ إِلَّا إِنَاثًا وَإِن يَدْعُونَ إِلَّا شَيْطَانًا مَّرِيدًا
Hausa
 
Bă su kiran kőwa, baicin Shi, făce mătă kuma bă su kiran kőwa făce Shaiɗan, mai tsaurin kai.

Ayah   4:118   الأية
لَّعَنَهُ اللَّهُ ۘ وَقَالَ لَأَتَّخِذَنَّ مِنْ عِبَادِكَ نَصِيبًا مَّفْرُوضًا
Hausa
 
Allah Yă la'ane shi. Kuma ya ce: "Lalle ne, ză ni riƙi rabő yankakke , daga băyinKa.

Ayah   4:119   الأية
وَلَأُضِلَّنَّهُمْ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمْ وَلَآمُرَنَّهُمْ فَلَيُبَتِّكُنَّ آذَانَ الْأَنْعَامِ وَلَآمُرَنَّهُمْ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلْقَ اللَّهِ ۚ وَمَن يَتَّخِذِ الشَّيْطَانَ وَلِيًّا مِّن دُونِ اللَّهِ فَقَدْ خَسِرَ خُسْرَانًا مُّبِينًا
Hausa
 
"Kuma lalle ne, ină ɓatar da su, kuma lalle ne ină sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dőmin su kătse kunnuwan dabbőbi, kuma lalle ne ină umurnin su dőmin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yă yi hasara, hasara bayyananniya.

Ayah   4:120   الأية
يَعِدُهُمْ وَيُمَنِّيهِمْ ۖ وَمَا يَعِدُهُمُ الشَّيْطَانُ إِلَّا غُرُورًا
Hausa
 
Yană yi musu alkawari, kuma yană sanya musu gũri, alhăli Shaiɗan bă ya yi musu wani wa'adĩn kőme face ruɗi.

Ayah   4:121   الأية
أُولَٰئِكَ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَلَا يَجِدُونَ عَنْهَا مَحِيصًا
Hausa
 
Waɗannan matattararsu Jahannama ce, kuma bă sămun makarkata daga gare ta.

Ayah   4:122   الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَنُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ وَعْدَ اللَّهِ حَقًّا ۚ وَمَنْ أَصْدَقُ مِنَ اللَّهِ قِيلًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, ză mu shigar da su gidăjen Aljanna (waɗanda) ƙőramu sună gudăna a ƙarƙashinsu, sună măsu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wăne ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?

Ayah   4:123   الأية
لَّيْسَ بِأَمَانِيِّكُمْ وَلَا أَمَانِيِّ أَهْلِ الْكِتَابِ ۗ مَن يَعْمَلْ سُوءًا يُجْزَ بِهِ وَلَا يَجِدْ لَهُ مِن دُونِ اللَّهِ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا
Hausa
 
(Al'amari) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma ba gũrace- gũracen Mutănen Littăfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki ză a săka masa da shi kuma bă zai sămi wani masőyi ba, baicin Allah, kuma bă zai sămi mataimaki ba.

Ayah   4:124   الأية
وَمَن يَعْمَلْ مِنَ الصَّالِحَاتِ مِن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَأُولَٰئِكَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ وَلَا يُظْلَمُونَ نَقِيرًا
Hausa
 
Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhăli kuwa Yană mũmini, to, waɗannan sună shiga Aljanna kuma bă ză a zălunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba.

Ayah   4:125   الأية
وَمَنْ أَحْسَنُ دِينًا مِّمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ لِلَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ وَاتَّبَعَ مِلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفًا ۗ وَاتَّخَذَ اللَّهُ إِبْرَاهِيمَ خَلِيلًا
Hausa
 
Kuma wăne ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhăli kuwa yană mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrăhĩm, Yană mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Yă riƙi Ibrăhĩm badăɗayi .

Ayah   4:126   الأية
وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ مُّحِيطًا
Hausa
 
Kuma Allah ke da (mallakar) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yă kasance, a dukkan, kőme, Mai kẽwayewa.

Ayah   4:127   الأية
وَيَسْتَفْتُونَكَ فِي النِّسَاءِ ۖ قُلِ اللَّهُ يُفْتِيكُمْ فِيهِنَّ وَمَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فِي الْكِتَابِ فِي يَتَامَى النِّسَاءِ اللَّاتِي لَا تُؤْتُونَهُنَّ مَا كُتِبَ لَهُنَّ وَتَرْغَبُونَ أَن تَنكِحُوهُنَّ وَالْمُسْتَضْعَفِينَ مِنَ الْوِلْدَانِ وَأَن تَقُومُوا لِلْيَتَامَىٰ بِالْقِسْطِ ۚ وَمَا تَفْعَلُوا مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِهِ عَلِيمًا
Hausa
 
Sună yi maka fatawa a cikin sha'anin mătă. Ka ce: "Allah Yană bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantăwa a kanku a cikin Littăfi, a cikin sha'anin marăyun mătă waɗanda ba ku bă su abin da aka rubũta musu (na gădo) ba, kuma kună kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yăra, da sha'anin tsayuwarku ga marăyu da ădalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yă kasance Masani a gare shi."

Ayah   4:128   الأية
وَإِنِ امْرَأَةٌ خَافَتْ مِن بَعْلِهَا نُشُوزًا أَوْ إِعْرَاضًا فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا أَن يُصْلِحَا بَيْنَهُمَا صُلْحًا ۚ وَالصُّلْحُ خَيْرٌ ۗ وَأُحْضِرَتِ الْأَنفُسُ الشُّحَّ ۚ وَإِن تُحْسِنُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرًا
Hausa
 
Kuma idan wata mace ta ji tsőron ƙiyo daga mijinta kő kuwa bijirẽwa to, băbu laifi a kansu su yi sulhu a tsakăninsu, sulhu (mai kyau) Kuma yin sulhu ne mafi alhẽri. Kuma an halartar wa rayũka yin rőwa. Kuma idan kun kyautata, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne, Allah Yă kasance, ga abin da kuke aikatăwa, Masani.

Ayah   4:129   الأية
وَلَن تَسْتَطِيعُوا أَن تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّسَاءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ ۖ فَلَا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوهَا كَالْمُعَلَّقَةِ ۚ وَإِن تُصْلِحُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Kuma bă ză ku iya yin ădalci ba a tsakanin mătă kő dă kun yi kwaɗayin yi. Sabőda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rătaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yă kasance Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah   4:130   الأية
وَإِن يَتَفَرَّقَا يُغْنِ اللَّهُ كُلًّا مِّن سَعَتِهِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ وَاسِعًا حَكِيمًا
Hausa
 
Kuma idan sun rabu, Allah zai wadătar da kőwanne daga yalwarSa. Kuma Allah Yă kasance Mayalwaci, Mai hikima.

Ayah   4:131   الأية
وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ وَلَقَدْ وَصَّيْنَا الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ وَإِيَّاكُمْ أَنِ اتَّقُوا اللَّهَ ۚ وَإِن تَكْفُرُوا فَإِنَّ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ غَنِيًّا حَمِيدًا
Hausa
 
Kuma Allah ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littăfi a gabăninku, da kũ, cẽwa ku bi Allah da taƙawa, kuma idan kun kăfirta, to, lalle ne, Allah Yană da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa. Kuma Allah Yă kasance wadătacce, Gődadde.

Ayah   4:132   الأية
وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ وَكِيلًا
Hausa
 
Kuma Allah ne da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa, kuma Allah Yă isa Ya zama wakĩli.

Ayah   4:133   الأية
إِن يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ أَيُّهَا النَّاسُ وَيَأْتِ بِآخَرِينَ ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ قَدِيرًا
Hausa
 
Idan Yă so, ză Ya tafi da ku, yă kũ mutăne! kuma Ya zo da wasu. Allah Yă kasance a kan haka, Mai ĩkon yi ne.

Ayah   4:134   الأية
مَّن كَانَ يُرِيدُ ثَوَابَ الدُّنْيَا فَعِندَ اللَّهِ ثَوَابُ الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ سَمِيعًا بَصِيرًا
Hausa
 
Wanda ya kasance Yană nufin sakamakon dũniya, to, a wurin Allah sakamakon dũniya da Lăhira yake. Kuma Allah Yă kasance Mai ji, Mai gani.

Ayah   4:135   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ بِالْقِسْطِ شُهَدَاءَ لِلَّهِ وَلَوْ عَلَىٰ أَنفُسِكُمْ أَوِ الْوَالِدَيْنِ وَالْأَقْرَبِينَ ۚ إِن يَكُنْ غَنِيًّا أَوْ فَقِيرًا فَاللَّهُ أَوْلَىٰ بِهِمَا ۖ فَلَا تَتَّبِعُوا الْهَوَىٰ أَن تَعْدِلُوا ۚ وَإِن تَلْوُوا أَوْ تُعْرِضُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرًا
Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku kasance măsu tsayuwa da ădalci, măsu shaida sabőda Allah, kuma kő dă a kanku ne kő kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kő a kansa) ya kasance mawadăci kő matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabőda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kő kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yă kasance Masani ga abin da kuke aikatăwa.

Ayah   4:136   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا آمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَالْكِتَابِ الَّذِي نَزَّلَ عَلَىٰ رَسُولِهِ وَالْكِتَابِ الَّذِي أَنزَلَ مِن قَبْلُ ۚ وَمَن يَكْفُرْ بِاللَّهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا
Hausa
 
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Ku yi ĩmăni da Allah da Manzonsa, da Littăfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littăfin nan wanda Ya saukar daga gabăni. To, wanda ya kăfirta da Allah da mală'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rănar Lăhira, to, lalle ne yă ɓace, ɓata mai nĩsa.

Ayah   4:137   الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا ثُمَّ آمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا ثُمَّ ازْدَادُوا كُفْرًا لَّمْ يَكُنِ اللَّهُ لِيَغْفِرَ لَهُمْ وَلَا لِيَهْدِيَهُمْ سَبِيلًا
Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmăni, sa'an nan kuma suka kăfirta, sa'an nan kuma suka yi ĩmani, sa'an nan kuma suka kăfirta sa'an nan kuma suka ƙăra kăfirci, Allah bai kasance Yană găfarta musu ba, kuma bă zai shiryar da su ga hanya ba.

Ayah   4:138   الأية
بَشِّرِ الْمُنَافِقِينَ بِأَنَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا
Hausa
 
Ka yi wa munăfukai bushăra da cẽwa lalle ne sună da azăba mai raɗaɗi.

Ayah   4:139   الأية
الَّذِينَ يَتَّخِذُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِ الْمُؤْمِنِينَ ۚ أَيَبْتَغُونَ عِندَهُمُ الْعِزَّةَ فَإِنَّ الْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا
Hausa
 
Waɗanda suke riƙon kăfirai masőya, baicin mũminai. Shin sună nẽman izza ne a wurinsu? To, lalle ne izza ga Allah take gabă ɗaya.

Ayah   4:140   الأية
وَقَدْ نَزَّلَ عَلَيْكُمْ فِي الْكِتَابِ أَنْ إِذَا سَمِعْتُمْ آيَاتِ اللَّهِ يُكْفَرُ بِهَا وَيُسْتَهْزَأُ بِهَا فَلَا تَقْعُدُوا مَعَهُمْ حَتَّىٰ يَخُوضُوا فِي حَدِيثٍ غَيْرِهِ ۚ إِنَّكُمْ إِذًا مِّثْلُهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ جَامِعُ الْمُنَافِقِينَ وَالْكَافِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا
Hausa
 
Kuma lalle ne Yă sassaukar muku a cikin Littăfi cẽwa idan kun ji ăyőyin Allah, ană kăfirta da su, kuma ană izgili da su, to, kada ku zauna tăre da sũ, sai sun shiga cikin wani lăbări. Lalle ne kũ, a lőkacin nan misălinsu kuke. Lalle ne, Allah Mai tăra munăfukai da kăfirai ne a cikin Jahannama gabă ɗaya.

Ayah   4:141   الأية
الَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمْ فَإِن كَانَ لَكُمْ فَتْحٌ مِّنَ اللَّهِ قَالُوا أَلَمْ نَكُن مَّعَكُمْ وَإِن كَانَ لِلْكَافِرِينَ نَصِيبٌ قَالُوا أَلَمْ نَسْتَحْوِذْ عَلَيْكُمْ وَنَمْنَعْكُم مِّنَ الْمُؤْمِنِينَ ۚ فَاللَّهُ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ وَلَن يَجْعَلَ اللَّهُ لِلْكَافِرِينَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ سَبِيلًا
Hausa
 
Waɗanda suke jiran dăko game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: "Ashe, ba mu kasance tăre da kũ ba?" Kuma idan wani rabo ya sămu ga kăfirai sai su ce: "Ashe ba mu rinjăye ku ba, kuma muka tsare ku daga mũminai?" To,Allah ne Yake yin hukunci tsakăninku a Rănar ˇiyăma, kuma Allah bă zai sanya hanya ba ga kăfirai a kan mũminai.

Ayah   4:142   الأية
إِنَّ الْمُنَافِقِينَ يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَهُوَ خَادِعُهُمْ وَإِذَا قَامُوا إِلَى الصَّلَاةِ قَامُوا كُسَالَىٰ يُرَاءُونَ النَّاسَ وَلَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
Lalle ne munăfukai sună yaudarẽwa da Allah, alhăli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tăshi zuwa ga salla, sai su tăshi sună măsu kasăla. Suna nũnawa mutăne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan.

Ayah   4:143   الأية
مُّذَبْذَبِينَ بَيْنَ ذَٰلِكَ لَا إِلَىٰ هَٰؤُلَاءِ وَلَا إِلَىٰ هَٰؤُلَاءِ ۚ وَمَن يُضْلِلِ اللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُ سَبِيلًا
Hausa
 
Măsu kai-kawo ne a tsakănin wancan; bă zuwa ga waɗannan ba, kuma bă zuwa ga waɗannan ba. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bă za ka sămar masa wata hanya ba.

Ayah   4:144   الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِ الْمُؤْمِنِينَ ۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَجْعَلُوا لِلَّهِ عَلَيْكُمْ سُلْطَانًا مُّبِينًا
Hausa
 
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku riƙi kăfirai masőya, baicin mũminai. Shin, kană nufin ku sanyă wa Allah dalĩli bayyananne a kanku?

Ayah   4:145   الأية
إِنَّ الْمُنَافِقِينَ فِي الدَّرْكِ الْأَسْفَلِ مِنَ النَّارِ وَلَن تَجِدَ لَهُمْ نَصِيرًا
Hausa
 
Lalle ne, manăfukai sună a magangara mafi ƙasƙanci daga wuta. Kuma bă ză ka săma musu mataimaki ba.

Ayah   4:146   الأية
إِلَّا الَّذِينَ تَابُوا وَأَصْلَحُوا وَاعْتَصَمُوا بِاللَّهِ وَأَخْلَصُوا دِينَهُمْ لِلَّهِ فَأُولَٰئِكَ مَعَ الْمُؤْمِنِينَ ۖ وَسَوْفَ يُؤْتِ اللَّهُ الْمُؤْمِنِينَ أَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyăra, kuma suka nẽmi fakuwa ga Allah, kuma suka tsarkake addininsu dőmin Allah, to, waɗannan sună tăre da mũminai, kuma Allah zai bai wa mũminai lăda mai girma.

Ayah   4:147   الأية
مَّا يَفْعَلُ اللَّهُ بِعَذَابِكُمْ إِن شَكَرْتُمْ وَآمَنتُمْ ۚ وَكَانَ اللَّهُ شَاكِرًا عَلِيمًا
Hausa
 
Mẽne ne Allah zai amfăna da yi maku azăba idan kun gőde, kuma kun yi ĩmăni? Allah Yă ksance Mai gődiya Masani.

Ayah   4:148   الأية
لَّا يُحِبُّ اللَّهُ الْجَهْرَ بِالسُّوءِ مِنَ الْقَوْلِ إِلَّا مَن ظُلِمَ ۚ وَكَانَ اللَّهُ سَمِيعًا عَلِيمًا
Hausa
 
Allah bă Ya son bayyanăwa da mũnăna daga magana făce ga wanda aka zălunta. Kuma Allah Yă kasance Mai ji, Masani.

Ayah   4:149   الأية
إِن تُبْدُوا خَيْرًا أَوْ تُخْفُوهُ أَوْ تَعْفُوا عَن سُوءٍ فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ عَفُوًّا قَدِيرًا
Hausa
 
Idan kun bayyana alhẽri, kő kuwa kuka ɓőye shi, kő kuwa kuka yăfe laifi daga cũta, to, lalle ne Allah Yă kasance Mai yăfewa, Mai ikon yi.

Ayah   4:150   الأية
إِنَّ الَّذِينَ يَكْفُرُونَ بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ وَيُرِيدُونَ أَن يُفَرِّقُوا بَيْنَ اللَّهِ وَرُسُلِهِ وَيَقُولُونَ نُؤْمِنُ بِبَعْضٍ وَنَكْفُرُ بِبَعْضٍ وَيُرِيدُونَ أَن يَتَّخِذُوا بَيْنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا
Hausa
 
Lalle ne, waɗanda uke kăfirta da Allah da ManzonSa kuma sună nufin su rarrabe a tsakănin Allah da manzanninSa, kuma sună cẽwa: "Mună ĩmăni da săshe, kuma mună kăfirta da săshe." Kuma sună nufin su riƙi hanya a tsakănin wannan.

Ayah   4:151   الأية
أُولَٰئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ حَقًّا ۚ وَأَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا مُّهِينًا
Hausa
 
Waɗannan sũ ne kăfirai sősai, kuma Mun yi tattali, dőmin kăfirai, azăba mai walăkantarwa.

Ayah   4:152   الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ وَلَمْ يُفَرِّقُوا بَيْنَ أَحَدٍ مِّنْهُمْ أُولَٰئِكَ سَوْفَ يُؤْتِيهِمْ أُجُورَهُمْ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa
 
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni da Allah da manzanninSa, kuma ba su rarrabe a tsakănin kőwa ba daga gare su, waɗannan ză Mu bă su ijărőrinsu, kuma Allah Yă kasance Mai găfara, Mai jin ƙai.

Ayah   4:153   الأية
يَسْأَلُكَ أَهْلُ الْكِتَابِ أَن تُنَزِّلَ عَلَيْهِمْ كِتَابًا مِّنَ السَّمَاءِ ۚ فَقَدْ سَأَلُوا مُوسَىٰ أَكْبَرَ مِن ذَٰلِكَ فَقَالُوا أَرِنَا اللَّهَ جَهْرَةً فَأَخَذَتْهُمُ الصَّاعِقَةُ بِظُلْمِهِمْ ۚ ثُمَّ اتَّخَذُوا الْعِجْلَ مِن بَعْدِ مَا جَاءَتْهُمُ الْبَيِّنَاتُ فَعَفَوْنَا عَن ذَٰلِكَ ۚ وَآتَيْنَا مُوسَىٰ سُلْطَانًا مُّبِينًا
Hausa
 
Mutănen Littăfi sună tambayar ka ka saukar da wani littăfi daga sama, a kansu, to, lalle ne sun tambayi Mũsă mũfă girma daga wannan, suka ce: "Ka nũna mana Allah bayyane." Sai tsăwa ta kămă su sabőda zăluncinsu, sa'an nan kuma suka riƙi maraƙi (abin bautăwa) băyan hujjoji bayyanannu sun je musu. Sa'an nan Muka yăfe laifi daga wancan. Kuma Mun bai wa Mũsă dalĩli bayyananne.

Ayah   4:154   الأية
وَرَفَعْنَا فَوْقَهُمُ الطُّورَ بِمِيثَاقِهِمْ وَقُلْنَا لَهُمُ ادْخُلُوا الْبَابَ سُجَّدًا وَقُلْنَا لَهُمْ لَا تَعْدُوا فِي السَّبْتِ وَأَخَذْنَا مِنْهُم مِّيثَاقًا غَلِيظًا
Hausa
 
Kuma Muka ɗaukaka dũtse săma da su, sabőda alkawarinsu, kuma Muka ce musu: "Ku shiga ƙőfar kună măsu tawăli'u," Kuma Muka ce musu: "Kada ku ƙẽtare haddi a cikin Asabat," kuma Muka riƙi alkawari mai kauri daga gare su."

Ayah   4:155   الأية
فَبِمَا نَقْضِهِم مِّيثَاقَهُمْ وَكُفْرِهِم بِآيَاتِ اللَّهِ وَقَتْلِهِمُ الْأَنبِيَاءَ بِغَيْرِ حَقٍّ وَقَوْلِهِمْ قُلُوبُنَا غُلْفٌ ۚ بَلْ طَبَعَ اللَّهُ عَلَيْهَا بِكُفْرِهِمْ فَلَا يُؤْمِنُونَ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa
 
To, sabőda warwarẽwarsu ga alkawarinsu, da kăfirtarsu da ăyőyin Allah, da kisansu ga Annabăwa, bă da hakki ba, da maganarsu: "Zukătanmu sună cikin rufi." Ă'a, Allah ne Ya yunƙe a kansu sabőda kăfircinsu, sabőda haka bă ză su yi ĩmăni ba făce kaɗan.

Ayah   4:156   الأية
وَبِكُفْرِهِمْ وَقَوْلِهِمْ عَلَىٰ مَرْيَمَ بُهْتَانًا عَظِيمًا
Hausa
 
Kuma sabőda kăfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma.

Ayah   4:157   الأية
وَقَوْلِهِمْ إِنَّا قَتَلْنَا الْمَسِيحَ عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ رَسُولَ اللَّهِ وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَٰكِن شُبِّهَ لَهُمْ ۚ وَإِنَّ الَّذِينَ اخْتَلَفُوا فِيهِ لَفِي شَكٍّ مِّنْهُ ۚ مَا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ إِلَّا اتِّبَاعَ الظَّنِّ ۚ وَمَا قَتَلُوهُ يَقِينًا
Hausa
 
Da faɗarsu : "Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsă ɗan Maryama Manzon Allah," alhăli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka săɓă wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sună shakka daga gare, shi, bă da wani ilmi făce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni.

Ayah   4:158   الأية
بَل رَّفَعَهُ اللَّهُ إِلَيْهِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا
Hausa
 
Ă'a, Allah Ya ɗauke shi zuwa garẽ Shi, kuma Allah Yă kasance Mabuwăyi, Mai hikima.

Ayah   4:159   الأية
وَإِن مِّنْ أَهْلِ الْكِتَابِ إِلَّا لَيُؤْمِنَنَّ بِهِ قَبْلَ مَوْتِهِ ۖ وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكُونُ عَلَيْهِمْ شَهِيدًا
Hausa
 
Kuma băbu kőwa daga Mutănen Littafi , făce lalle yană ĩmăni da shi a gabănin mutuwarsa, kuma a Rănar ˇiyăma yana kasancẽwa mai shaida, a kansu.

Ayah   4:160   الأية
فَبِظُلْمٍ مِّنَ الَّذِينَ هَادُوا حَرَّمْنَا عَلَيْهِمْ طَيِّبَاتٍ أُحِلَّتْ لَهُمْ وَبِصَدِّهِمْ عَن سَبِيلِ اللَّهِ كَثِيرًا
Hausa
 
To, sabőda zălunci daga waɗanda suka tũba (Yahũdu) Muka haramta musu abũbuwa masu dăɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma sabőda taushẽwarsu daga hanyar Allah da yawa.

Ayah   4:161   الأية
وَأَخْذِهِمُ الرِّبَا وَقَدْ نُهُوا عَنْهُ وَأَكْلِهِمْ أَمْوَالَ النَّاسِ بِالْبَاطِلِ ۚ وَأَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ مِنْهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا
Hausa
 
Da karɓarsu ga riba, alhăli kuwa an hana su daga gare ta, da cin su ga dũkiyar mutăne daƙarya. Kuma Muka yi tattali, dőmin kăfirai, azăba mai raɗaɗi.

Ayah   4:162   الأية
لَّٰكِنِ الرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ مِنْهُمْ وَالْمُؤْمِنُونَ يُؤْمِنُونَ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ ۚ وَالْمُقِيمِينَ الصَّلَاةَ ۚ وَالْمُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَالْمُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ أُولَٰئِكَ سَنُؤْتِيهِمْ أَجْرًا عَظِيمًا
Hausa
 
Amma tabbatattu a cikin ilmi daga gare su, da mũminai, suna ĩmani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabăninka, madalla da masu tsai da salla, da măsu băyar da zakka, da măsu ĩmăni daAllah da Rănar Lăhira. Waɗannan ză Mu bă su lăda mai girma.

Ayah   4:163   الأية
إِنَّا أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ كَمَا أَوْحَيْنَا إِلَىٰ نُوحٍ وَالنَّبِيِّينَ مِن بَعْدِهِ ۚ وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالْأَسْبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَارُونَ وَسُلَيْمَانَ ۚ وَآتَيْنَا دَاوُودَ زَبُورًا
Hausa
 
Lalle ne Mu, Mun yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabăwa daga băyansa. Kuma Mun yi wahayi zuwa ga Ibrăhĩma da Ismă'ĩla da Is'hăƙa da Yaƙũbu da jĩkőki da ĩsa da Ayũba da Yũnusa da Hăruna da Sulaimăn. Kuma Mun bai wa Dăwũda zabũra.

Ayah   4:164   الأية
وَرُسُلًا قَدْ قَصَصْنَاهُمْ عَلَيْكَ مِن قَبْلُ وَرُسُلًا لَّمْ نَقْصُصْهُمْ عَلَيْكَ ۚ وَكَلَّمَ اللَّهُ مُوسَىٰ تَكْلِيمًا
Hausa
 
Da wasu Manzanni, haƙĩ ƙa, Mun bă da lăbarinsu a gare ka daga gabăni, da wasu manzanni waɗanda ba Mu bă da lăbărinsu ba a gare ka, kuma Allah Yă yi magana da Mũsă, magana sősai.

Ayah   4:165   الأية
رُّسُلًا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى اللَّهِ حُجَّةٌ بَعْدَ الرُّسُلِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا
Hausa
 
Manzanni măsu băyar da bushăra kuma măsu gargaɗi dőmin kada wata hujja ta kasance ga mutăne a kan Allah băyan Manzannin. Kuma Allah yă kasance Mabuwăyi, Mai hikima.

Ayah   4:166   الأية
لَّٰكِنِ اللَّهُ يَشْهَدُ بِمَا أَنزَلَ إِلَيْكَ ۖ أَنزَلَهُ بِعِلْمِهِ ۖ وَالْمَلَائِكَةُ يَشْهَدُونَ ۚ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ شَهِيدًا
Hausa
 
Amma Allah Yană shaida da abin da Ya saukar zuwa gare ka. Yă saukar da shi da saninSa. Kuma mală'iku sună shaida. Kuma Allah Yă isa Ya zama shaida.

Ayah   4:167   الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَصَدُّوا عَن سَبِيلِ اللَّهِ قَدْ ضَلُّوا ضَلَالًا بَعِيدًا
Hausa
 
Lalle ne, waɗanda suka kăfirta kuma suka kange (wasu mutăne) daga hanyar Allah, haƙĩƙa, sun ɓace, ɓata mai nĩsa.

Ayah   4:168   الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَظَلَمُوا لَمْ يَكُنِ اللَّهُ لِيَغْفِرَ لَهُمْ وَلَا لِيَهْدِيَهُمْ طَرِيقًا
Hausa
 
Lalle ne waɗanda suka kăfirta, kuma suka yi zălunci, Allah bai kasance Yana yi musu găfara ba, kuma bă Ya shiryar da su ga hanya.

Ayah   4:169   الأية
إِلَّا طَرِيقَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرًا
Hausa
 
Făce hanyar Jahannama, sună măsu dawwama a cikinta har abada, kuma wannan yă kasance, ga Allah, mai sauƙi.

Ayah   4:170   الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءَكُمُ الرَّسُولُ بِالْحَقِّ مِن رَّبِّكُمْ فَآمِنُوا خَيْرًا لَّكُمْ ۚ وَإِن تَكْفُرُوا فَإِنَّ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Hausa
 
Yă kũ mutăne! Haƙĩƙa, Manzo yă je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabőda haka ku yi ĩmăni yă fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kăfirta, to, Allah Yană da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yă kasance Masani, Mai hikima.

Ayah   4:171   الأية
يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَا تَغْلُوا فِي دِينِكُمْ وَلَا تَقُولُوا عَلَى اللَّهِ إِلَّا الْحَقَّ ۚ إِنَّمَا الْمَسِيحُ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ رَسُولُ اللَّهِ وَكَلِمَتُهُ أَلْقَاهَا إِلَىٰ مَرْيَمَ وَرُوحٌ مِّنْهُ ۖ فَآمِنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ ۖ وَلَا تَقُولُوا ثَلَاثَةٌ ۚ انتَهُوا خَيْرًا لَّكُمْ ۚ إِنَّمَا اللَّهُ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۖ سُبْحَانَهُ أَن يَكُونَ لَهُ وَلَدٌ ۘ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ وَكَفَىٰ بِاللَّهِ وَكِيلًا
Hausa
 
Yă Mutănen Littăfi! Kada ku zurfafă a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, făce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yă jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabőda haka, ku yi ĩmăni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, "Uku". Ku hanu (daga faɗin haka) yă fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yă tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yă isa Ya zama wakĩli.

Ayah   4:172   الأية
لَّن يَسْتَنكِفَ الْمَسِيحُ أَن يَكُونَ عَبْدًا لِّلَّهِ وَلَا الْمَلَائِكَةُ الْمُقَرَّبُونَ ۚ وَمَن يَسْتَنكِفْ عَنْ عِبَادَتِهِ وَيَسْتَكْبِرْ فَسَيَحْشُرُهُمْ إِلَيْهِ جَمِيعًا
Hausa
 
Masĩhu bă ya ƙyămar ya kasance băwa ga Allah, kuma haka mală'ikun nan makusanta. Kuma wanda ya yi ƙyămar bautarSa kuma yi yi girman kai, to, zai tăra su zuwa gare shi gabă ɗaya.

Ayah   4:173   الأية
فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَيُوَفِّيهِمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضْلِهِ ۖ وَأَمَّا الَّذِينَ اسْتَنكَفُوا وَاسْتَكْبَرُوا فَيُعَذِّبُهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا وَلَا يَجِدُونَ لَهُم مِّن دُونِ اللَّهِ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا
Hausa
 
To, amma waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to ză Ya cika musu ijărőrinsu, kuma Yană ƙăra musu daga falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyăma, kuma suka yi girman kai, to, ză Ya yi musu azăba, azăba mai raɗɗi kuma bă su samun wani masőyi dőmin kansu, baicin Allah, kuma bă su samun mataimaki.

Ayah   4:174   الأية
يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءَكُم بُرْهَانٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَأَنزَلْنَا إِلَيْكُمْ نُورًا مُّبِينًا
Hausa
 
Yă kũ mutăne! Haƙĩƙa wani dalĩli daga Ubangijinku yă je muku kuma Mun saukar da wani haske, bayyananne zuwa gare ku.

Ayah   4:175   الأية
فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَاعْتَصَمُوا بِهِ فَسَيُدْخِلُهُمْ فِي رَحْمَةٍ مِّنْهُ وَفَضْلٍ وَيَهْدِيهِمْ إِلَيْهِ صِرَاطًا مُّسْتَقِيمًا
Hausa
 
To, amma waɗanda suka yi ĩmăni da Allah kuma suka faku a gare Shi, to, zai shigar da su cikin wata rahama daga gare Shi da wata falala, kuma Ya shiryar da su zuwa gare Shi ga tafarki madaidaici.

Ayah   4:176   الأية
يَسْتَفْتُونَكَ قُلِ اللَّهُ يُفْتِيكُمْ فِي الْكَلَالَةِ ۚ إِنِ امْرُؤٌ هَلَكَ لَيْسَ لَهُ وَلَدٌ وَلَهُ أُخْتٌ فَلَهَا نِصْفُ مَا تَرَكَ ۚ وَهُوَ يَرِثُهَا إِن لَّمْ يَكُن لَّهَا وَلَدٌ ۚ فَإِن كَانَتَا اثْنَتَيْنِ فَلَهُمَا الثُّلُثَانِ مِمَّا تَرَكَ ۚ وَإِن كَانُوا إِخْوَةً رِّجَالًا وَنِسَاءً فَلِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنثَيَيْنِ ۗ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ أَن تَضِلُّوا ۗ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
Hausa
 
Sună yi maka fatawa. Ka ce: "Allah Yană bayyana muku fatawa a cikin 'Kalăla."' Idan mutum ya halaka, ba shi da, rẽshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gădon ta, idan wani rẽshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ('yan'uwa mătă) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mătă to namiji yana da misălin rabon mătă biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, dőmin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kőme. 
 


© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us